Gwamnatin jihar Sokoto ta jajanta wa 'yan'uwan mutanen da suka rasu./Hoto:Gwamnatin Jihar Sokoto

Mutum bakwai 'yan gida ɗaya sun mutu sakamakon cin abinci mai guba a ƙaramar hukumar Shagari da ke jihar Sokoto a arewa maso yammacin Nijeriya.

Mutanen sun mutu ne bayan sun ci rogo mai ɗauke da guba a ƙauyen Runjin Barmo, a cewar wata sanarwa da Nura Bello, mai magana da yawun Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta jihar ya fitar a ranar Lahadi.

Sanarwar ta ƙara da cewa Dagacin ƙauyen, Muhammadu Modi, wanda ya tabbatar wa Kwamishinar Lafiya ta jihar Hajiya Asabe Balarabe aukuwar lamarin, ya ce mutanen sun ci rogon ne da daddare lamarin da ya yi ajalinsu.

“Mutanen da suka mutu su ne Abubakar da matarsa da 'ya'yansu biyar,” in ji sanarwar.

Ɗaya daga cikin 'ya'yan, wanda shi ne na shida cikin waɗanda suka ci rogon, bai mutu ba, kamar yadda sanarwar ta bayyana.

Hajiya Asabe ta ce an tura jami'ai gwamnati ƙauyen domin tattaro bayanai kan abin da ya faru don miƙa wa gwamnati kafin ta ɗauki mataki.

Kwamishinar ta ce ma'aikatarta za ta ɗauki samfur daga jikin yaron da ya tsallake rijiya da baya domin yin gwaje-gwajen kimiyya da zummar gano aihini dalilin rasuwar mutanen.

Gwamnatin jihar Sokoto ta miƙa ta'aziyya ga wa 'yan'uwan mutanen da suka rasu tare da fatan ganin hakan bai sake aukuwa ba.

TRT Afrika