Nijeriya ta ƙara sanya ido a duk hanyoyin shiga ƙasar don hana yaɗuwar cutar Farankamar Biri

Nijeriya ta ƙara sanya ido a duk hanyoyin shiga ƙasar don hana yaɗuwar cutar Farankamar Biri

Mummunar cutar Farankamar Biri mai saurin yaduwa na haifar da barna a yankuna da dama na Afirka.
Muhammad Ali Pate

Ministan Lafiya na Nijeriya Farfesa Muhammad Ali Pate ya jaddada cewa ƙasar ta ƙarfafa sa ido da tantancewa a duka hanyoyin shiga ƙasar a ƙoƙarinta na hana yaɗuwar cutar Farankamar Biri wato Mpox, Clade 1 da ake fargabarta.

Mummunar cutar Farankamar Biri mai saurin yaduwa na haifar da barna a yankuna da dama na Afirka.

Hakan ya sa Hukumar Lafiya ta Duniya ta ayyana ta a matsayin Annobar Lafiya ta Duniya, wadda ke bukatar daukar matakan gaggawa da hadin kai na kasa da kasa don dakile yaduwarta da rage tasirinta.

A sanarwar da Ma’aikatar Lafiyar ta fitar a ranar Alhamis, Farfesa Pate ya bayyana cewa Hukumar Daƙile Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Nijeriya (NCDC) a karkashin ma’aikatar lafiya da jin dadin jama’a ta tarayya, sun dauki matakin karfafa tsaron Nijeriya tun kafin lokacin ayyana Mpox a matsayin Annobar Lafiya ta Duniya da Hukumar Dakile Cututtuka Masu Yaduwa ta Afirka ta yi.”

Wannan nau'in Mpox Clade 1 ya haifar da asarar rayuka a cikin kusan kashi 10% na mutanen da suka kamu da rashin lafiya a barkewar annobar da ta gabata.

Ministan ya ƙara da cewa makasudin shi ne a magance tare da rage tasirinta ta hanyar amfani da matakan da aka yi amfani da su yayin bala'in COVID-19.

Farfesa Pate ya ci gaba da bayanin cewa gwamnati ta aiwatar da wani sabon umarni da ke bukatar duk matafiya da su cika fom din ayyana lafiya ta intanet kafin su tashi zuwa kasar.

An bullo da wannan matakin ne tare da kaddamar da cibiyoyin kula da cututtuka a dukkan jihohi 36 da kuma babban birnin tarayya.

Ministan ya kuma shawarci al’umma da su rika tsafta da yawaita wanke hannu da sabulu da ruwa, ko kuma amfani da sinadarin tsaftace hannu, musamman bayan haɗuwa da mai cutar ko taɓa dabba.

Ana yada MPOX ta hanyar mu’amala ta ƙut-da-ƙut kamar jima'i, hulɗar fata-da-fata, da magana ko numfashi kusa da wani.

Mece ce mpox

Mpox cuta ce da ake ɗauka daga ƙwayar cutar bairos. Kuma alamunta su ne zazzaɓi, da ciwon kai da ciwon baya da ciwon gaɓoɓi da kasala da yawan gajiya da kumburi.

Ƙuraje za su iya fesowa su kuma watsu a gaba ɗayan jiki, sai dai suna fin yawa a fuska, sannan daga baya su bushe su riƙa ɓarewa daga jiki.

Ƙwayar cutar mpox na janyo rashin lafiya a mafi yawan lokuta. Alamunta za su iya bayyana tsakanin kwana biyar zuwa 21 bayan kamuwa.

Ya take yaɗuwa?

Ƙwayar cutar za ta iya yaɗuwa idan mutum ya taɓa mai ɗauke da cutar ko ya taɓa wani abin da mai cutar ya taɓa ya kuma gurɓata shi.

Sai dai haɗarin yaɗa cutar ga jama’a ba shi da yawaƘwayar cutar ta fi kama yara kuma zuwa kaso goma cikin ɗari na waɗanda suka kamu da mpox za su iya mutuwa.

A ina ake samun mpox?

Cutar Mpox ta samo asali ne daga dazuzzuka a ƙasashe masu zafi a Tsakiya da Yammacin Afirkakuma tana yaɗuwa tsakanin dabbobin daji.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta ce har yanzu ba a gano ‘ainihin inda mpox take tasowa ba’ sai dai ƙwayar cutar ta fi yaɗuwa ne a tsakanin ɓeraye da birrai.

A ina aka fara gano mpox?

An fara gano cutar a 1958 bayan cuta mai kama da ƙyanda ta ɓarke a cikin birai da aka yi amfani da su wajen bincike.

An fara gano cutar a jikin mutane a Jamhuriyar Dimokuraɗiyyar Kongo a 1970A ranar 13 ga Agusta, Cibiyar Yaƙi da Cututtuka Masu Yaɗuwa ta bayyana cutar a matsayin annoba a duka faɗin nahiyar.

A lokacin da ƙwayar cutar ta mpox nau’in clab 1b mai haɗari da saurin yaɗuwa a baya ta yaɗu daga Jamhuriyar Dimukuraɗiyyar Kongo zuwa iyakokin ƙasashe maƙota kamar Burundi da Kenya da Rwanda Uganda.

Shin akwai maganin cutar?

A yanzu dai babu wani takamemen maganin mpox. Akwai riga-kafi uku da ake da su da kuma a Janairun 2022 Hukumar Magunguna ta Turai ta amince a yi amfani da wani magani da aka samar na cutar agana don jinyar mpox, sai dai bai wadata ba a cikin jama’a.

Hukumar Yaƙi da Cutuka Masu Yaɗuwa ta Nijeriya (NCDC) ta ce akwai matakan da za a iya ɗauka a matsayin riga-kafin cutar, waɗanda suka haɗa da:

  • Nisantar duk dabbodin da ke iya yaɗa cutar da suka haɗa da marasa lafiya da mushe a wuraren da aka samu mpox
  • Da nisantar duk wani abu da dabbar da ba ta da lafiya ta taɓa
  • Killace dabbobin da aka ga alamun sun kamu da cutar, kada su haɗu da sauran dabbobi.
  • Dafa naman dabbobi da ƙwansu da nononsu sosai kafin a ci ko a sha
  • Keɓe mutanen da suka kamu, da kuma saka kayan kariya duk lokacin da za a je wajensu
  • Wanke hannu a-kai-a-kai bayan kula ko ziyartar marasa lafiya
  • Wayar da kan mutane kan cutar da matakan kariya.

TRT Afrika