DRC tana da adaɗi mafi yawa na mutanen da suka kamu da cutar Mpox, yanayin da haifar da damuwa a duniya game da yaduwar cutar. Hoto: AP

Kongo za ta karɓi kashin farko na alluran rigakafin don taƙaita yaduwar cutar ƙyandar biri wato Mpox a mako mai zuwa daga Amurka, kamar yadda Ministan Lafiya na ƙasar ya bayyana a ranar Litinin.

Hakan na zuwa kwanaki kaɗan bayan Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ayyana ɓarkewar cutar a matsayin barazana.

An tabbatar da barkewar cutar a tsakanin yara da manya a ƙasashen Afirka fiye da goma, sannan sabon nau'in ƙwayar cutar na yaduwa sosai, kazalika ana fama da ƙarancin alluran rigakafin cutar a nahiyar.

DRC tana da adadi mafi yawa na mutanen da suka kamu da cutar Mpox, kana tana buƙatar allurar rigakafi miliyan uku a halin yanzu.

Amurka da Japan sun yi tayin bayar da gudunmawar allurar rigakafin, kamar yadda Ministan Lafiya na ƙasar Roger Kamba ya shaida wa manema labarai.

Ko da yake dai bai bayyana adadin yawan allurar ko kuma lokacin da ƙasar Japan za ta aika da nata ba.

Sabon nau'in cutar

A rahoton da Hukumar WHO ta fitar, ta ce sama da mutum 17,000 ne suka kamu da cutar sannan mutum 500 ne suka mutu sakamakon cutar a faɗin duniya a wannan shekara.

Sama da kashi 96 cikin 100 na wadanda suka kamu da cutar da wadanda suka mutu sun fito ne daga Kongo, ƙasar da tsarin kiwon lafiyarta ya daɗe yana fuskantar koma baya wajen dakile barkewar cututtuka a fadin ƙasar da kuma rashin ababen more rayuwa.

Yara 'yan kasa da shekaru 15 ne suka ɗauki kaso sama da 70 cikin kashi 85 na mace-macen da aka samu a Kongo, kazalika masana kimiyya sun nuna damuwarsu game da sabon nau'in cutar mpox a Kongo wanda za a iya yaɗa shi cikin sauƙi.

A makon da ya gabata, Sweden ta bayyana samun rahoton bullar sabon nau'in cutar a ƙasar.

Sabbin alamomin cutar

Sabanin sauran nau'in cutar Mpox na baya, inda aka fi ganin guraje a kan ƙirji da hannaye da kuma ƙafafu, sabon nau'in cutar yana haifar da ƙananan cututtuka da ƙuraje a kan al'aura.

Wannan yanayin yana da matukar wahalar ganewa, ma'ana mutane na iya yaɗa cutar ba tare da sun sani ba.

Ba ta iska ake ɗaukar cutar ba, yawanci dai ana buƙatar kusancin fata da fata wajen ƴaɗuwarta.

Hukumar ta WHO ta ce, a karon farko an gano cutar mpox ne a kasashen yankin gabashin Afirka hudu da suka hada da Burundi da Kenya da Rwanda da kuma Uganda, sannan baki ɗaya an danganta su da barkewar cutar a Kongo.

AP