Zuwa yanzu girgizar kasar ta yi sanadin mutuwar fiye da mutum 2,100. Hoto: Reuters

Masu aikin ceto a ranar Litinin sun dukufa a kokarinsu na tono mutanen da ake tsammanin suna da rai da baraguzai ya danne su a kauyukan da ke yankin tsaunin Atlas na Maroko, kwana uku bayan afkuwar mummunar gigizar kasar da ba a taba ganin irinta ba a kasar.

Girgizar kasar mai girman maki 6.8 da ta faru a ranar Juma'a da marece a yankin kudu maso yammacin birnin Marrakech, ta yi sanadin mutuwar fiye da mutum 2,100 tare da jikkata sama da mutum 2,400, mafi yawansu kuma munanan raunuka suka ji, kamar yadda alkaluman hukumomi suka nuna a ranar Lahadi da yamma.

A ranar Lahadi gwamnatin kasar da ke birnin Rabat ta sanar da cewa ta amince da karbar tayin taimako daga kasashen hudu, yayin da wasu kasasehn da dama su ma suka nuna bukatar son aika wa da taimako.

An karbi tayin taimakon kasashe hudu

Hukumomi sun amsa tayin da aka yi musu daga kasashen Sifaniya da Birtaniya da Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa "a wannan matakin, na aika wa da tawagogin masu aikin agaji," in ji Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida ta Moroko.

Ta ce tawagogin kasashen wajen suna magana da hukumomin Moroko don tsara yadda abubuwa za su gudana, inda ta ce a yanzu tayi hudu kawai aka karba saboda "rashin tsara komai yadda ya dace zai iya jawo cikas."

Mai yiwuwa a karbi tayin sauran kasashen a nan gaba "idan bukatar hakan ta taso," a cewar ma'aikatar.

A shirye Faransa take ta bayar da taimako idan Moroko ta sake bukatar hakan, in ji Shugaba Emmanuel Macron.

Wani jirgin Qatar dauke da kayan agaji ya bar sansanin jiragen sama na Al Udeid da ke wajen birnin Doha a ranar Lahadi da yamma, a cewar kamfanin dillancin labarai na AFP.

Sifaniya ta aika masu aikin ceto 86 da karnuka takwas da aka yi wa horo kan gano abu zuwa Maroko don "taimaka wa wajen neman wadanda suke da sauran kwana a karkashin baraguzai sakamakon girgizar kasar da ta faru a makwabciyar kasarmu," kamar yadda sanarwar Ma'aikatar Tsaron Kasar ta fada.

"Za mu aika da duk abin da ake bukata saboda kowa ya san cewa wadannan sa'o'in na farko suna da muhimmanci, musamman idan akwai mutanen da baraguzai ya danne kuma ba su mutu ba," kamar yadda Ministar Tsaro ta Sifaniya Margarita Robles ta fada a wani jawabi da ta yi a talabijin.

Kauyuka sun rushe sun zama turbaya

Girgizar kasar ta rushe kafatnin kauyukan da ke kan tsaunukan Atlas inda masu aikin ceto na sa kai da a rundunar sojin Moroko suke ta faman tono wadanda ba su mutu ba da kuma gawarwakin wadanda suka mutu.

Gidajen kauyukan da dama ginin laka ne da tabo.

Kauyen Tafeghaghte mai nisan kilomita 60 daga from Marrakech a gundumar Haouz y lalace baki daya, kamar yadda wata tawagar AFP ta ruwaito, inda ta ce gidaje kadan ne bas u rushe ba.

“Mun rasa komai! Mun shiga uku. Ba abin da ke min dadi,” Zahra Benbrik mai shekara 62 wacce ta rasa ‘yan’uwanta 18 ta fada tana kuka.

Hukumomi sun ce mutum fiye da 1,300 ne suka mutu a gundumar Al Haouz kawai. Gidan talabijin na kasar Maroko ya ce “fiye da iyalai 18,000 abin ya shafa,” a yankin Al Haouz, inda nan ne abin ya fi Kamari.

Ma’aikatar Ilimi ta sanar da cewa an dakatar da komawa makaranta a kauyukan da ke yankin Al Haouz a ranar Litinin.

AFP