Gidan wanka na Hammam da ke Hebron mai shakara 240 na bayar da ayyuka masu kayatarwa ga jama'a. / Hoto: Reuters

Tsawon shekaru, Fatima Mhattar na marabtar masu sayar da kayayyaki, dalibai, ma'aikatan banki da 'yan fansho a gidan wanka na Hammam El Majd, wani gidan wankan jama'a a wajen Rabat babban birnin Morokko.

Suna shiga dakin zafi da na tiriri, sannan a mitsittsike musu jikkunansu, a wanke su da soso da sabulu tare da abokai da makotansu.

Gidajen wankan - Hammam da Larabci - tsawon karni da dama sun kasance wani bangare na rayuwar jama'ar Morokko.

Mata da maza, masu hannu da shuni da talakawa na iya zuwa gidajen wankan.

Masu wanka na zama a kan dandamalin duwatsu da suke kan tayil masu ado, sannan sai a yi musu wanda da wani bakin sabulu na gargajiya da ruwan dumi da aka kawo a bokitai.

Hammam, matsalolin baya-bayan nan

Amma wadannan gidajen wanka sun zamo masu sanya damuwa a kwanakin nan, sakamkon yadda Moroko ta dauki shekaru tana fama da karancin ruwan sama, abin da mahukunta suka kira da babban ibtila'i.

Garuruwan da ke kasar ta Arewacin Afirka sun wajabta lallai gidajen wanka na Hammam su dinga rufe wa na tsawon kwanaki uku a mako a wannan shekarar, domin tattalin ruwan da ake da shi

Mhattar ta yi murmushi a yayin da take gaisawa da wasu iyalai da ke bukatar bokitai cike da zannuwan wanka, takalma su waje da saura kayan wanka da aka kawo Hamma din a ranar Lahadi.

Amma ta damu kan yadda wannan sabuwar doka za ta janyo raguwar masu zuwa wanka wanda zai rage kudaden da take samu.

"Ko a ranakun da aka bude na Alhamiz zuwa Lahadi, mafi yawan jama'a na ƙin zuwa saboda suna tsoron wajen na iya ciia nda jama'a,' in ji Mhattar.

Karancin ruwan sama da yanayi mai zafi sosai ya karar da ma'ajiyar ruwa ta Moroko, hakan na tsoratar da manoma da garuruwan Moroko da suka dogara kan albarkatun ruwa.

Kasar na gabatar da zabi masu wahala ga jama'a, yayin da take duba tasirin fari da sauyin yanayi.

Tattalin arzikin Hammam

Matakin da aka dauka na takaita ayyukan wasu masu sana'a da suka hada da Hammam da wuraren wanke mota ya bakantawa wasu rai.

Masu zuwa gidajen wankan da 'yan siyasa na bayyana cewar gwamnati na yin ba daidia ba, saboda ba ta samar da daidaiton amfani da ruwana wuraren da aka fi amfani da su irin su gidajen hotel, wuraren ninkaya, ko a bangaren ayyukan noma na kasar wanda ke shanye sama da rabin ruwan Morokko.

"Wannan mataki ba zai zama wani mai amfanarwa ba, musamman tunda dai bangaren gidajen wankan ba ya daya daga cikin bangarorin da suke amfani d ruwan Moroko da yawa," in ji Fatima Zahra Bata, mamban majalisar wakilai ta Moroko, a yayin a take tambayar Ministan Harkokin Cikin Gida Abdelouafi Laftit a wata rubutacciyar wasika a watan da ya gabata.

Bata ta tambayi me ya sa jami'ai a garuruwa da dama suka ware wuraren gyaran jiki na Spa daga matakin da suka dauka, wanda 'yan yawon bude idosuke amfai da shi.

Ta yi gargadi da cewa rufe gidajen wanka na Hammam zai kara rauni da whaalar da masu sana'ar ke ciki, wadanda kudaden da suke samu a wata bai wuce dirham 2,000 zuwa 3,000 ba. Ma'aikatan Hammam na samun dala 200 zuwa dala 300.

Wannan mataki na rufe gidajen wanka ya shafi kusan mutane 200,000 kai tsaye da suka mallaka ko aiki a wuraren, wanda suke amfani da kaso biyu cikin dari na ruwan d aake da shi a kasar, kamar yadda Hukumar Kididdiga ta Morokko ta sanar.

An rufe gidajen wanka na Hammam a garuruwan da suka hada da Casablanca da Tangier da Beni Mellal tun lokacin da MinistanHarkokin Cikin Gida, ya nemi jami'an yankin da su aiwatar da matakan tattalin ruwa a farkon wannan shekara.

Tare da tashin farashin gas din girki da saukar zafi, rufe gidajen wankan ya janyo damuwa ta musamman a garuruwan da ke yankin tsaunukan Atlas inda mutane ke zuwa Hammam don wanke jikkunansu.

Mustapha Baradine, wni kafinta a Rabat, na son zuwa Hammam a kai a kai da iyalinsa, kuma bai fahimci yadda dan ruwan da yake amfani da shi zai yi tasiri ga karancin ruwan sama ba.

A ra'ayinsa, wannan hani na janyo bacin rai da kuma kawo tambayar arziki, matsayi da mulki.

"Ina amfani da bokiti biyu me kawai na ruwa don wanka tare da yarana," in ji shi. "Ba na son wannan mataki da aka dauka sam. Zai fi zama abu mai kyau idan har za su karar da ma'ajiyar ruwansu," ya fada yana mai nufin ma'aikatan yankunan.

Abubuwan da maƙwabtan Maroko ke yi

Morokko ta rage yaduwar talauci a 'yan shekarun nan, amma rashin daidaito wajen samun kudade na ci gaba da daduwa a kauyuka da birane.

Duk da samun cigaban tattalin arziki cikin hanzari a wasu bangarorin, marasa galihi sun dinga gudanar da zanga-zanga kan bambanci da tsadar rayuwa.

Makotan Morokko sun zabi daidaita amfani da ruwa a bangarori daban-daban.

A Tunisia, an tirsasa wa jama'a rufe dukkan fanfunansu an tsawon awanni a kowacce rana.

A wani bangare na kasar Spaniya, an hana jama'a wanke motoci, cika wuraren wanka da ruwa da baiwa fulawowi ruwa a bazarar da ta gabata.

Fatima fedouachi, shugabar masu gidajen wanka na Hammam a Casablanca ta ce rufe gidajen wankan ya janyo sauyi kan yadda suke gudanar da ayyukansu.

Duk da kungiyar masu giudajen wankan ba ta fitar da alkaluma kan asarar da take yi ba, amma sun yi gargadi kan illar da matakin zai kawo ga sana'arsu da ma ma'aikatansu.

Fedouachi ta ce "Ya zama tilas masu gidajen wanka su yi abun da ya kamata ga masu zuwa wanka."

Har a ranakun da aka ce mu rufe wuraren wankan, mafi yawan Hammam na ci gaba da kona gawayi don kar wurin ya yi sanyi, maimakon su bar su haka kawai, in ji ta.

Ta ce mamallaka sun fi aminta da a bude kullum amma a raba awanin ga gidajen wanka daban-daban,

Wasu masu zuwa Hammam na cewa wannan rufe wa na wayar da kan jama'a kan fari da karancin ruwa da ake fuskanta.

Masu zuwa wankan a koyaushe irin su Hanane Al Mossaid na goyon bayan wannan mataki a fadin kasar.

El Moussaid ta ce "Idan babu isasshen ruwa, gara na sha maimakon na je Hammam."

TRT Afrika