Bala'in ya shafi yawancin tituna da gidaje a Western Cape. / Hoto: Getty Images

Afirka ta Kudu ta sanar da shiga shirin ko-ta-kwana na Kwamitin Magance Bala'i a Western Cape, bayan da aka yi gargaɗin yiwuwar faruwa mummunar ambaliya a yankin ranar Litinin.

Cibiyar kula da yanayi ta Afirka ta Kudu ta fitar da gargaɗin mataki na tara, kan yiwuwar ambaliya, inda hakan ya sanya hukumomi suka rufe makarantu ranar Litinin.

An saka jami'an agaji cikin shiri, kuma hukumomi sun ce, iska mai ƙarfi ta yi ta'adi a faɗin yankin cikin ƙarshen mako, kuma ta ɓaɓɓake rufin gidaje da kayar da bishiyu.

Yawancin tituna da gidajen Gundumar Moqhaka, sun faɗa cikin ambaliyar, sakamakon mamakon ruwan sama da ya shafi unguwannin Kroonstad da Maokeng, cewar rahotanni daga SABC na Afirka ta Kudu.

Kakakin unguwar Dika Kheswa ya faɗa wa 'yan jarida a yankin cewa gundumar ba za ta iya tantance yawan ta'adin ba a yanzu.

An shawarci mazauna yankin su guje wa wuraren da ke kwari da kuma gadoji.

Hukumomin sun ƙara da cewa ƙaƙƙarfar iska ce ta haddasa gobara kusan 40 a yankin, cikinsu har da gobarar da ta lamushe kusan bukkoki 300, kuma ta shafi kusan mutane 2,000 zuwa yanzu.

TRT Afrika