Ana fargabar za a shafe kimanin mako biyu ana tsananin zafi a ƙasar. / Hoto: Getty Images

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta sanar da cewa za ta rufe duka makarantun ƙasar daga ranar Litinin sakamakon tsananin zafin da ake fargabar ƙasar za ta fusakanta.

Ma’aikatun ilimi da na lafiya sun bayar da shawara ga iyayen yara kan yara su zauna a gida sakamakon ana fargabar zafi a ƙasar zai kai har maki 45 a ma’aunin Celsius.

Ma’aikatun sun yi gargaɗi kan cewa duk wata makaranta da aka kama a buɗe za ta fuskanci hukunci wanda hakan zai iya kaiwa ga har a ƙwace lasisinta.

Duk da cewa ma’aikatun ba su sanar da tsawon lokacin da makarantun za su kasance a rufe ba, amma hasashen yanayi ya nuna cewa za a shafe kusan mako biyu ana fuskantar wannan zafin.

Ma'aikatun sun ce za su ci gaba da sanya ido kan lamarin tare da sanar da jama'a yadda ya kamata.

Peter Garang, wani mazaunin Juba babban birnin kasar, ya yi maraba da matakin.

Ya ce “ya kamata a saka wutar lantarki a makarantu” domin a samu damar shigar da na’urorin sanyaya ɗaki.

Sudan ta Kudu wadda tana daga cikin sabbin ƙasashe a duniya, na fama da matsalar sauyin yanayi tare da tsananin zafi na gama gari amma ba kasafai yake kai maki 40 ba a ma’aunin Celcius.

Rikicin cikin gida dai ya addabi kasar da ke gabashin Afirka wadda ita ma take fama da fari da ambaliyar ruwa, lamarin da ya jefa mazauna kasar cikin wahala.

AP