'Yan sanda sun haramta zanga-zangar da shugaban 'yan adawa Raila Odinga ya kira Photo/ AP Archive

‘Yan sanda a Kenya na cikin shirin ko-ta-kwana a daidai lokacin da shugaban ‘yan adawa na kasar, Raila Odinga ya ce za a gudanar da zanga-zanga kan gwamnatin Shugaba William Ruto kan batun tsadar rayuwa.

A wani sako da ya bayyana a shafinsa na Tuwita, Odinga ya kira da a fito zanga-zanga a ranar Litinin da Alhamis duk da haramcin da ‘yan sanda suka saka.

Ko a makon da ya gabata sai da abubuwa suka tsaya cik a Nairobi babban birnin kasar bayan zanga-zanga ta rikide zuwa tarzoma.

An kashe wani dalibin jami’a a lokacin da aka yi arangama tsakanin masu zanga-zangar da kuma ‘yan sandan kwantar da tarzoma, inda aka raunata ‘yan sanda 31.

‘Yancin zanga-zanga

An tsaurara tsaro a ranar Litinin, inda kuma aka girke ‘yan sandan kwantar da tarzoma a muhimman wurare a Nairobi babban birnin Kenya, an rufe shaguna sannan an dakatar da sufurin motocin haya da na jiragen kasa.

Wani mai sharhi kan siyasa, Martin Ambati ya bayyana cewa ‘yancin yin zanga-zanga cikakken ‘yanci ne ga duk wani dan Kenya kamar yadda kundin tsarin mulkin kasar ya tanada.

“Babban sufeton ‘yan sanda ba shi da wani karfi kuma ba zai iya kwace karfin da kundin tsarin mulki ya bayar ba. Ba zai iya fin karfin kundin tsarin mulki ba,” kamar yadda Ambati ya shaida wa TRT Afrika.

Akwai dumbin mutane a Kenya da ke fuskantar wahalhalu da suka shafi samar wa kansu da iyalansu abincin da za su ci sakamakon hauhawar farashin kayayyakin abinci da kuma karewar darajar kudin kasar da mummunan fari da ya jefa miliyoyi cikin yunwa.

TRT Afrika