Ƙaramin Ministan Tsaron Nijeriya Bello Matawalle da Babban Hafsan Sojojin ƙasar da sauran shugabannin sojoji za su tare a Jihar Sokoto don fatattakkar Bello Turji da sauran ‘yan ta’adda da ke addabar mutane a Arewa Maso Yammacin ƙasar.
Minista Bello Matawalle ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da Daraktan Watsa Labarai da Hulɗa da Jama’a na Ma’aikatar Tsaron ƙasar Henshaw Ogubike Minor ya fitar ranar Asabar da daddare.
“Ƙaramin ministan ya damu da yadda ‘yan ta’adda da ɓarayin daji suke addabar jihohin Sokoto da Zamfara da Katsina da Kebbi da maƙotansu,” a cewar sanarwar.
Ta ƙara da cewa wannan ne ya sa ministan ya umarci Babban Hafsan Tsaron ƙasa da sauran shugabannin sojoji su tafi Sokoto - wacce ita ce hedkwatar sojoji ta Sokoto da Zamfara da Katsina da Kebbi - tare da shi, a matsayin wani yunƙuri na kakkaɓe ta’addanci da garkuwa da mutane daga yankin.
A lokacin da suke yankin na arewa maso yamma, “Za su sa ido kan ayyukan soja don tabbatar da cewa an gama da Bello Turji da tawagarsa,” in ji sanarwar.
A wannan makon da ke ƙarewa ne aka ringa yaɗa wani bidiyo da ke nuna Bello Turji da yaransa ɗauke da bindigogi suna kwashe makamai daga wata motar yaƙi ta sojoji a cikin daji, sannan suka cinna mata wuta suna murna.
Sanarwar ma’aikatar tsaron ta Nijeriya ta ce motar sojojin ta maƙale ne a wani yanki mai caɓi cikin dare, “shi ya sa daga baya aka umarci sojojin da suke cikin motar su bar wajen, saboda kada a kai musu farmaki.”
Lamarin dai ya faru ne a ƙauyen Kwashabawa a ƙaramar hukumar Zurmi ta jihar Zamfara, kamar yadda sanarwar ta nuna.
“Lokacin ɓarayin nan na daji da ‘yan ta’adda ya ƙare, domin zafafa ayyukan da za a yi ba ƙaƙƙautawa zai illata su,” a cewar sanarwar ta ma’aikatar tsaro.
Sanarwar ta ƙara da cewa gwamnatin tarayya ta damu ƙwarai da barazanar da 'yan ta'adda suke yi, musamman a yankin Arewa Maso Yamma.
Minista Bello Matawalle ya ce a shirye gwamnati take ta ɗauki duk matakin da ya dace don tabbatar da cewa an fatattaki masu aikata laifukan, an kuma dawo da zaman lafiya a garuruwa.
“Da ni da Babban Hafsan Tsaron Nijeriya da sauran shugabannin sojoji za mu kasance a can, muna jagorantar sojojinmu,” a cewar Bello Matawalle.