Wani yaro da yaƙi da raba da gidansu a Sudan yana ɗiban ruwa a sansanin Zamzam, a Arewacin Darfur a Sudan, ranar 1 ga Agustan 2004. / Hoto: Reuters Archive

Majalisar Ɗinkin Duniya (MDD) tana neman dala biliyan shida saboda Sudan a wannan shekara daga ƙungiyoyin ba da agaji na duniya don rage wahalar da ake sha a abin da ta kira ɗaya daga mafi munin matsalar da aka fuskanta a duniya, matsalar da take ƙara ƙamari saboda yadda mutane suka barin gidajensu da kuma ƙaruwar yunwa.

Roƙon na MDD na ranar Litinin na nufin ƙarin sama da kaso arba’in daga abin da aka nemar wa Sudan a bara, a daidai lokacin da kasafin kuɗin tallafi a duka faɗin duniya ke raguwa, sakamakon dakatar da tallafi daga Amurka kamar yadda Shugaba Donald Trump ya sanar a watan jiya, abin da kuma ya shafi shirye-shiryen ceto rayuka a faɗin duniya.

Sai dai MDD ta ce dole ne a samar da kuɗin saboda tasirin yaƙin da aka shafe watanni 22 ana yi tsakanin sojojin Sudan da mayaƙan RSF - wanda tuni ya raba kaso ɗaya cikin biyar na al’ummar Sudan da gidajensu, ya kuma haifar da matsananciyar yunwa ga rabin mutanen ƙasar - ke nuna alamun zai ƙara ƙamari.

“Lamarin Sudan wata babbar matsala ce da bil’adama yake ciki mai tayar da hankali.” a cewa Babban Jami’i mai Jagorantar Agajin Majalisar Ɗinkin Duniya Tom Fletcher, gabanin ƙaddamar da neman tallafin. “Yunwa tana ƙara ƙamari. Ana samun mastalar cin zarafi ta hanyar jima’i. Ana kashe yara ana jikkata su. Wahalar da ake sha tsananta.”

An bayar da rahoton muguwar yunwa a aƙalla yankuna biyar na Sudan, ciki har da sansanin waɗanda suka bar gidansu a Dafur, a cewar sanarwar MDD, inda ta ƙara da cewa lamari zai ƙara muni, yayin da ake ci gaba da faɗa da kuma rugujewar muhimman kayan buƙatun rayuwa.

Dakarun RSF sun kai hari ɗaya daga sansanonin da yunwar ta fi addaba a makon jiya, yayin da mayaƙan suke ƙoƙarin riƙe Dafur, wajen da ta fi ƙarfi.

Yayin da wasu hukumomin bayar da agaji suke cewa Amurka ta bari su ci gaba da ba tallafi a Sudan, har yanzu akwai rashin tabbas kan wuraren da za a kai tallafin.

Shirin na MDD yana so ya kai ga mutane miliyan 21 a ƙasar, abin da ya sa ya zama shirin neman agaji mafi girma a 2025 kawo yanzu, kuma ake neman dala biliyan 4.2 - ragowar kuma za a yi amfani da shi ne don waɗanda yaƙi ya raba da gidajensu.

TRT World