Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa "yaƙin da ake yi a Sudan zai haifar da matsalar yunwa mafi muni a duniya" yayin da ƴan kasar da suka maƙale "suna tsere da lokaci" don shawo kan matsalar ƙarancin abinci da ake fuskanta.
Ɗaruruwan manoma sun kaurace wa yin aiki a gonakinsu masu albarka, lamarin da ya haifar da rashin girbi da kuma tsananta matsalar barazanar yunwa da ake fuskanta, a cewar wani sabon rahoto da MDD ta fitar.
Eddie Rowe, daraktan hukumar samar da abinci ta duniya a Sudan, ya ce ƙasar na fama da ƙarancin abinci na kashi 41 cikin ɗari idan aka kwatanta da bara, inda alƙaluma suka nuna yankuna kamar Darfur na fama da ƙarancin abinci da ya kai kashi 78 cikin ɗari.
“Matsakaicin ƴan Sudan ba su da ƙarfin saye abinci,'' kamar yadda Rowe ya shaida wa kamfanin dillancin labaran AFP inda ya ce kashi 60 cikin 100 na al'ummar ƙasar suna aiki ne a fannin noma kuma ma’aikatan gwamnati ba sa karɓar albashi a yanzu haka.
"Kusan mutane miliyan biyar suna kwana da yunwa," in ji shi.
Tsawaita lokacin yaki
Yaƙi ya barke a shekarar da ta gabata tsakanin rundunar sojin Sudan da ke ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙasar Abdel Fattah al-Burhan da kuma dakarun rundunar RSF da tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo ke jagoranta.
Yaƙin ya yi sanadin mutuwar dubun dubatar mutane tare da tilasta wa miliyoyi ƙaurace wa matsugunansu, yanayin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta kira da "rikicin gudun hijira mafi girma a duniya."
Kazalika yaƙin ya haifar da tsananin ƙarancin abinci da kuma rashin jinƙai da ya jefa al'ummar ƙasar da ke arewa maso gabashin Afirka cikin barazanar yunwa.
''Akwai al'ummomi masu rauni da dama a ko'ina da ke buƙatar tallafi, '' a cewar Rein Paulsen, daraktan ayyukan gaggawa da jinƙai na Hukumar Abinci da Aikin Noma ta MDD.
'Kwana da yunwa'
Kashi 37 cikin 100 na gonaki ne kawai ake iya nomawa a duk faɗin ƙasar Sudan a yanzu, a cewar cibiyar bincike ta Fikra.
A yankin Al-Jazira da ke da yawan albarkatun ƙasa, tuni yaƙin ya yi sanadin lalacewar kadada 250,000 ta gonakin da ba a amfani da su, yanayin da ya yi sanadiyar kashe kusan kashi 70 cikin 100 na alkama na tan 800,000 da ƙasar ke nomawa a duk shekara.
"Muhimmin yanayin lokacin noma da shuka yana tafe nan da ƴan makonni. Watan Yuni shi ne muhimmin watan da manoma suke shuga a tsirai a cikin shekara,'' in ji Paulsen.
"Yana da matukar muhimmaci mu gaggauta shigar da kayayyaki da dama ... yanzu a hannun manoma domin ba su damar yin noma," in ji shi.
Bukatar 'Gaggawa'
Noman abinci ya tsaya cak, yayin da aka katse dukkan hanyoyin da ke zuwa tashar iyakokin Sudan, ''babbar hanyar shiga.''
"Mafi yawan kamfanonin da ke rarraba takin zamani da magungunan kashe kwari a rufe suke," a cewar Mohammed Suleiman, wani manomin masara daga jihar Gedaref da ke yankin gabashin ƙasar.
Yaƙin -- wanda masana suka yi gargaɗin cewa zai iya shafe tsawon wasu shekaru ana yi -- ya jefa ƴan Sudan miliyan 18 cikin mawuyacin hali na rashin abinci, waɗanda miliyan biyar daga cikinsu ke fuskantar barazanar tsananin yunwa.
A farkon watan nan ne ƙasashen duniya suka yi alƙawarin ba da tallafin sama da Euro biliyan biyu ga Sudan, rabin adadin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce ake buƙata, a yayin wani taro a birnin Paris.