Majalisar Ɗinkin Duniya ta ba da tallafin dala miliyan 100 ga ƙasashe 10 da ke fama da matsalolin jinƙai a nahiyar Afirka da Amurka da Asiya da kuma yankin Gabas ta Tsakiya, in ji majalisar a ranar Juma'a.
Sama da kashi uku na wannan tallafi zai tafi ne ga ayyukan jinƙai a Yemen, wadda za ta samu ($20 miliyan) sai Habasha (dala miliyan 15) sakamakon yadda mutane suke fama da yunwa da ƙaura da kuma cututtuka da bala'o'i na yanayi, in ji mai magana da yawun MDD a taron majalisar da aka saba gudanarwa.
Sauran kasashen da za su ci gajiyar tallafin sun haɗa da Myanmar wadda za ta samu (dala miliyan 12), sai Mali (dala miliyan 11) da Burkina Faso (dala miliyan 10) da Haiti (dala miliyan 9) da Kamaru (dala miliyan 7) da Mozambique (dala miliyan 7), da kuma Burundi ($5 miliyan) wadda iftila'in sauyin yanani na El Nino shafa sai kuma Malawi (dala miliyan 4).
''Muna matukar buƙatar ƙarin masu ba da taimako cikin gaggawa ga ƙasashen nan da ke fama tashe-tashen hankula da matsalolin jin ƙai" in ji jami'ar hukumar jinƙai ta OCHA Joyce Msuya.