Shugaban Hukumar da ke Hasashen Yanayi ta Majalisar Dinkin Duniya Petteri Taalas ya ce za a iya kauce wa asarar rayuka idan da a ce an fitar da gargadi kafin afkuwar al'amarin a kasar da yaki ya lalata. Hoto: AP

Majalisar Dinkin Duniya (MDD) tana bukatar fiye da dala miliyan 71 don taimaka wa wadanda ke cikin mawuyacin hali bayan mummunar ambaliyar ruwa ta mamaye Libya a karshen mako.

Mahaukaciyar guguwar da aka wa lakabi da Daniel ta ratsa ta Libya ne a ranar 10 ga watan Satumba, inda ta kashe mutum 11,300, kamar yadda Kungiyar Agaji ta Red Crescent a Libya ta bayyana.

A ranar Alhamis Hukumar Agaji ta Majalisar Dinkin Duniya UN OCHA ta ce ana hasashen adadin zai karu.

Ambaliyar ruwan ta fi shafar birnin Derna, wato wajen da wasu madatsun ruwa biyu suka fashe a yankin a ranar Lahadi. Kazalika ambaliyar ta shafe birnin Sousse.

Hukumar UN OCHA ta ce kaso 30 cikin 100 na birnin ya lalace kuma hanyoyin mota sun lalace yayin da mahukunta a yankin suke kira da a samar da hanyar kai musu agaji da kwashe jama'a.

Hukumar ta bayyana abin da "mummunan bala'i", ta ce kungiyoyin agaji suna bukatar dala miliyan 71.4 don su taimaka wa "mutane masu tsananin bukata su 250,000 cikin mutum 884,000 da ke bukatar taimako."

A ranar Laraba, Shugaban Hukumar UN OCHA Martin Griffiths ya sanar da kafa asusun gaggawa na dala miliyan 10.

"Ambaliyar ta shafe garuruwa da dama. Kazalika iyalai gaba daya ruwan ya tafi da su," kamar yadda ya bayyana a wata sanarwa.

"Samar da kayayyakin ceton rai ga mutane, zai magance matsalar lafiyar da za ta iya fada musu zuwa gaba, kuma hakan ya shafe duk wani abu mai muhimmanci a wannan matsanancin lokaci da Libya ta fada."

Bala'i a Derna

Amurka da Tarayyar Turai da Turkiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa (UAE) da wasu kasashe sun riga sun tura taimakonsu yayin da aka aika da tawagogin agaji don ceto wadanda ke da sauran numfashi da kuma gano gawawwaki.

"Cikin 'yan dakikoki yawan ruwan ya karu sosai," kamar yadda wani da ya tsira da ya samu rauni ya ce, ya ce ruwan ya tafi da mahaifiyarsa a tsakar dare kafin su samu su gudu zuwa cikin wani daki da ke kasan benensu."

"Ruwa ya ci gaba da karuwa a inda muke har sai bayan da muka hau hawa na hudu na benen, ruwan ya mamaye hawa na biyu," kamar yadda mutumin ya bayyana yayin da yake kwance a gadon na asibiti, Cibiyar Kiwon Lafiya ta Benghazi ce ta wallafa labarinsa.

"Mun rika jiyo ihu. Daga taga na hango motoci da gawawwaki da ruwa ya tafi da su. Ruwan ya kwashe tsawon sa'a ko sa'a daya da rabi — amma mu a wajenmu, gani muke kamar an yi shekara."

Daruruwan gawawwaki ne aka jera a titukan Derna suna jiran a yi musu jana'iza, yayin da dangi da 'yan uwa wadanda suke cikin kaduwa suka rika bin gine-gine suna neman 'yan uwansu da suka bace kuma manyan motoci sun share tarkace da kasa daga kan tituna.

"Bala'in ya yi ta'adi sosai, abin ya yi muni matuka," in ji Yann Fridez shugaban wakilan Kungiyar Agaji ta Red Cross wadda take da tawaga a Derna yayin da aka yi ambaliyar ruwan ta faru.

AFP