Mata suna karbar albashi kasa da na maza da kaso 34.2 cikin 100 a kasar Ghana, kamar yadda alkaluman Hukumar Kididdigar Kasar Ghana (GSS) kan kudin shigar iyalai na watanni hudu na farkon shekara suka bayyana.
Wadannan bayanai an bayyana su ne a daidai lokacin da ake Ranar Samar da Daidaito Tsakanin Maza da Mata a Duniya – ana bikin ranar ne a kowace ranar 18 ga watan Satumba don karfafa daidaito a wajen biyan ma'aikata.
Kiyasin bambancin ya danganta da shekaru da shekarun kwarewa da zurfin ilimi da aikin mutum da fannin da yake aiki da yankin da yake zama.
Kamar yadda alkaluman hukumar GSS suka bayyana, ana samun bambanci sosai wajen albashi a tsakanin ma'aikata da ke manyan makarantu, inda mata suke karbar albashi kasa da na maza da kaso 12.7 cikin 100.
Ko da yake an fi samun wagegen gibi a tsakanin ma'aikatan masu rike da shaidar karatun firamare da na sakadanre (da kaso 60.1 cikin 100) daga nan sai ma'aikata da ba su da ilimi (da kaso 54 cikin 100).
Dangane da bangaren da ma'aikata ke aiki, alkaluman sun ce bangaren kananan kamfanoni da 'yan kasuwa nan ne aka fi samun bambanci wajen biyan albashi tsakanin maza da mata, mata suna karbar albashi kaso 58.7 cikin 100 kasa da abin da takwarorinsu maza ke karba.
Daga nan sai bangaren ma'aikatan manyan kamfanoni masu zaman kansu mai bambancin kaso 29.9 cikin 100 tsakanin maza da mata.
Ko da yake a bangaren ma'aikatan gwamnati mata suna karbar albashi kaso 10.5 cikin 100 kasa da abin da maza ke karba, wanda shi ne gibi mafi kankanta.
A tsakanin al'umma mutane masu shekara 36 zuwa 60, ana biyan mata da ke wannan rukunin shekaru kasa da maza da kaso 33.4 cikin 100.
Hakan yana nufin akwai bambancin maki uku wanda shi ne mafi yawa a rukunin shekaru tsakanin shekara 15 zuwa 35, inda ake biyan mata kaso 30.7 cikin 100 kasa da maza.
Ko da yake bambancin albashi tsakanin ma'aikata maza da mata ya fi yawa tsakanin ma'aikatan masu takardar firamare da na sakandare da kaso (60.1 cikin 100) daga nan saii ma'aikata marasa karatu masu bambancin kaso 54 cikin 100 a tsakanin maza da mata.