Jami'an tsaro sun kashe ɗaruruwan 'yan Boko Haram  tun bayan da suka ƙara ƙaimi a yaƙin da suke yi da ƙungiyar.  / Hoto: Reuters

Mayaƙan ƙungiyar Boko Haram goma sha biyar sun yi saranda ga sojojin Nijeriya ranar Lahadi, a cewar wata sanara da rundunar sojin ta fitar.

Sanarwar ta ƙara da cewa rundunar sojin ta ƙaddamar da wani gagarumin samame a yankin Aguata da ke jihar Borno da ke arewa maso gabashin ƙasar.

Ta ce mayaƙa 15 na ƙungiyar sun yi saranda sakamakon samamen sannan an lalata maɓoyarsu.

Boko Haram ta ƙaddamar da kai hare-hare a arewa maso gabashin Nijeriya tun 2009, inda ta kashe dubban mutane tare da raba miliyoyi da muhallansu.

Tun 2015, ƙungiyar ta riƙa kai hare-hare a ƙasashe maƙwabtan Nijeriya irin su Kamari, Chadi da Jamhuriyar Nijar.

Sai dai dubban mayaƙan Boko Haram sun miƙa wuya sannan jami'an tsaro sun kashe ɗaruruwa tun bayan da suka ƙara ƙaimi a yaƙin da suke yi da ƙungiyar.

AA