Akalla sojojin Chadi 15 ne suka mutu sannan wasu 32 suka jikkata a wata arangamar da aka yi tsakanin sojojin da mayakan Boko Haram a ranar Asabar, a cewar wata sanarwa ta sojin ƙasar.
Mai magana da yawun rundunar sojin ta Chadi Janar Issakh Acheikh ya bayyana cewa su ma sojojin ƙasar sun kashe mayaƙan Boko Haram ɗin 96 da jikkata 11 da ƙwace makamansu a ranar Asabar.
Sai dai janar ɗin bai ba da cikakken bayani dangane da farmakin ko kuma inda lamarin ya faru.
“Rundunar sojin tana ƙara jaddada wa al’ummar Chadi cewa, tana ƙokarin shawo kan lamarin, kuma za a ci gaba da aikin gano inda sauran ɓaragurbin suke a wani bangare na aikin Operation Haskanite,'' in ji Acheikh, yana mai nuni da farmakin da sojojin suka kaddamar domin fatattakar mayakan Boko Haram daga tafkin Chadi.
Yankin dai ya sha fama da hare-haren ta’addanci waɗanda suka hada da na ƙungiyar IS a yammacin Afirka da kuma na 'yan Boko Haram, wanda ya barke a Arewa maso Gabashin Nijeriya tun daga shekarar 2009 ya kuma bazu zuwa yammacin ƙasar Chadi.
Kimanin sojoji 40 ne aka kashe a wani hari da aka kai a wani sansanin soji da ke yankin tafkin Chadi a karshen watan da ya gabata, bayan haka kuma shugaban rikon kwarya Mahamat Idriss Deby ya yi barazanar janye sojojin ƙasarsa daga rundunar tsaro na ƙasa da ƙasa.
Chadi ta kasance babbar abokiya ga dakarun Faransa da Amurka waɗanda ke neman taimakawa wajen yaki da ayyukan ta'addancin da aka kwashe tsawon shekaru 12 ana fama da shi a yankin Sahel na yammacin Afirka.
Yankin na Sahel na daga cikin wuraren da ke fuskantar hare-haren masu iƙirarin jihadi musamman a ƙasashen Nijar da Nijeriya da Chadi da Mali da Burkina Faso.