Da dama daga cikin likitocin kan fita kasashen waje ne saboda rashin samun ingantaccen yanayin aiki  Photo: Reuters / Photo: AFP

Majalisar dokokin Nijeriya ta yi karatu na biyu ga kudurin dokar da zai tilasta wa likitoci yin aiki a kasar na akalla shekara biyar kafin a ba su lasisi.

Kudurin, wanda dan majalisa Ganiyu Johnson daga jihar Legas ya gabatar ranar Alhamis, ya bukaci a yi gyara ga dokar ma'aikatan kiwon lafiya ta 2004.

Hakan zai sa ba za a bai wa duk wani likita da ya samu horo a Nijeriya cikakken lasisin soma aiki ba sai ya yi aiki na akalla shekaru biyar a kasar.

Dan majalisar ya ce matakin yana da muhimmanci a yayin da ake nuna fargaba game da yadda likitoci suke ta yin tururuwar fita daga kasar.

Daya daga cikin 'yan majalisar wakilan kuma kwararren likita, Dakta Yusuf Tanko Sununu ya shaida wa TRT Afrika cewa matakin da suke son dauka yana da muhimmanci sosai ganin yadda likitoci ke guduwa kasashen waje.

Ya kara da cewa duk da yake akwai matsaloli da dama da ke sanya likitocin kasar ficewa daga cikinta, ya kamata a dauki matakin magance hakan don guje wa rushewar fannin lafiya.

Ya ce ‘’Babu wani tanadi da aka yi wa likitan da ya kammala aikin horo, balle ya samu tabbacin cewa za a ba shi aiki a Nijeriya.

A cewarsa, majalisar za ta gudanar da taron jin ba'asin jama'a da zummar shawo kan matsalolin da ke sanya likitoci ficewa daga kasar.

A watan Agustan 2022, Kungiyar Likitocin Nijeriya NMA ta ce fannin kiwon lafiya kasar zai durkushe idan ba a dauki matakin gaggawa ba na dakatar da likitoci daga ficewa daga kasar.

TRT Afrika