Gwamantin jihar Filato ta sha alwashin kawo karshen hare-hare a jihar:Hoto/Facebook/CalebMuftwang

Wasu mutane da ke zanga-zanga sun cinna wuta a gidan Michal Monday Adanchi, hakimin garin Bokkos da ke karamar hukumar Bokkos a jihar Filato ta tsakiyar Nijeriya.

Ganau da kuma rundunar 'yan sandan Filato sun tabbatar wa TRT Afrika cewa lamarin ya faru ne da dazu da rana.

An gudanar da zanga-zangar ce bayan hukumomi sun kama mutum takwas da ake zargi da hannu a hare-haren da aka kai a wasu kauyukan Bokkos a lokacin Kirsimeti, a cewar ganau.

Sun ce bayan an kama mutanen ne mata ‘yan garin Bokkos suka fita domin nuna rashin jin dadinsu kuma suka je fadar basaraken suna zarginsa da hannu a kamen.

Sun kona gida tare da fadan basaraken jim kadan bayan sun isa fadan nasa, in ji shaidun.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Filato, Alabo Alfred, ya tabbatar wa TRT da faruwar lamarin, sai dai ya ce suna tattara bayanai ne domin fitar da sanarwa.

Ranar Alhamis ne dai rundunar ‘yan sandan jihar ta tabbatar da kama mutum takwas da ake zargi da hannu a hare-haren da aka kai kananan hukumomin Bokkos da Barkin Ladi a ranar jajibiren Kirsimeti.

Hare-haren dai sun shafi kauyuka 23 inda aka kashe mutum kusan dari biyu.

TRT Afrika