An shafe kusan wata uku ana rikici tsakanin sojojin Sudan da rundunar RSF. Hoto/AA

Ana zargin dakarun rundunar RSF ta Sudan da kai hari wani karamin kauye inda suka rinka harbe-harbe da kuma sace kayayyaki, lamarin da mazauna garin suka kira da “ta’ddanci” ga jama’a.

Kusan wata uku, rundunar RSF wadda Mohamed Hamdan Daglo ke jagoranta ta yi ta yaki da rundundar sojin kasar a karkashin jagorancin Abdel Fattah al-Burhan a rikicin da ya yi sanadin mutuwar akalla mutum 3,000 da kuma raba miliyoyi da muhallansu.

Rundundar RSF “na sata a bankuna da gine-ginen al’umma” a Bara, mai nisan kilomita 50 daga El-Obeid, babban birnin Arewacin Kordofan, kamar yadda wani da ya shaida lamarin a ranar Juma’a ya bayyana.

“Ana ta yi mana ta’ddanci: suna harbe-harbe da sata, kuma babu inda za ka ga soja ko dan sanda,” kamar yadda wani mazaunin garin Abdelmohsen Ibrahim ya bayyana.

“Ko da sojojin sun yi kokarin zuwa El-Obeid, RSF din ne ke da iko da titin El-Obeid zuwa Bara.”

El-Obeid na da nisan kilomita 350 daga Khartoum daga kudu, kuma wani wuri ne mai muhammanci kuma na kasuwanci, kuma yana da filin jirgi da manyan gidajen ajiye kayayyakin abinci.

Rikici na kara zafafa

Rikicin da aka soma tun 15 ga watan Afrilu ya fi kamari ne a Khartoum babban birnin Sudan da kuma Arewacin Kordofan da kuma yammacin Darfur inda a nan ne Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin yiwuwar “aikata laifukan yaki”.

A ranar Juma’a, mazauna sun bayar da rahoton arangama da ‘yan bindiga a birnin Omdurman da ke gefen Kogin Nilu.

Wadanda suka shaida lamarin sun kuma bayar da rahoton “hare-hare ta sama a yankin hedikwatar kafar watsa labarai ta Omdurman da kuma luguden wuta da bindigar kakkabo jirgi domin dakile harin” na sama.

Wani mutum ya sake bayyana cewa an kai hari ta sama kan sansanin RSF da ke arewacin Khartoum.

Akwai fararen hula da dama da suka zargi RSF da cin zarafinsu inda kuma suke bayyana cewa sojojin kasar ba su taka rawar gani domin ba su kariya ba.

Tun bayan da yakin ya barke, RSF ta yi ta kafa sansanoni a wuraren da jama’a ke zama inda ita kuma rundunar sojin kasar ta yi ta kokarin amfani da damar da take da ita ta jirgin sama domin kai hari ga RSF.

Asalin RSF

Ana zargin RSF da tilasta wa jama’a barin gidajensu da kwace musu motoci da cin zarafin mata ta hanyar lalata a daidai lokacin da suke guduwa zuwa garuruwa masu makwaftaka.

Kungiyar RSF ta samo asali ne daga mayakan Janjaweed – mayakan da suka aikata laifuka daban-daban ga kabilun da ba Larabawa ba a Darfur tun daga 2003.

Rikicin da ake yi a halin yanzu an ta yin yarjejeniyar tsagaita wuta inda wasu suka yi aiki da dama kuma aka yi ta sabawa, duk da shiga tsakani da kasashen duniya da na Afirka ke yi.

AFP