Wani masallaci mai dadadden tarihi a birnin Bole na kasar Ghana ya rushe.
Masallacin wanda wasu rahotanni ke cewa ya shafe sama da shekara 400 ya rushe sakamakon ruwan sama mai karfi da aka yi a makon jiya.
Kamfanin dillancin labarai na Ghana ya ce baya ga rushewar masallacin, ruwan saman ya karya babbar gadar da ke gundumar ta Bole.
Masallacin na Bole wanda yake kama da shahararren masallacin nan na Larabanga da ke Yammacin Gonja a yankin Savannah, an gina shi da laka da itace.
Tun da farko kafafen watsa labarai sun ruwaito cewa masallacin Larabanga ne ya rushe sakamakon kama da yake da na Bole, sai dai bincike ya nuna cewa yana nan bai rushe ba.
Wasu rahotanni na cewa an gina masallacin na Bole tun a karni na 16, sai dai wasu na cewa bai kai haka tsufa ba.
Ruwan sama mai karfi a ‘yan kwanakin nan ya yi barna a wurare da dama Ghana inda ya jawo ambaliya a wasu wurare.
Ko a cikin watan nan sai dai ambaliya ta shafi wasu sassa na Accra babban birnin Ghana.
Haka kuma kwanaki biyu kafin haka daruruwan mutane sun rasa muhallansu sakamakon igiyar ruwa wadda ta jawo ambaliya a garuruwan Keta da Anloga wadanda ke gabar teku a yankin Volta na Ghana.