Ministan Harkokin Wajen Turkiyya Hakan Fidan ya tattauna da gwamnatin Nijar kan yaƙi da ta'addanci a ziyarar da ya kai ƙasar, yana mai cewa ta'addanci "shi ne babban abin da ke haddasa rashin zaman lafiya a yankin Sahel."
"Mun tattauna kan abubuwan da suka kamata a yi a fannin ci gaban ayyukan tsaro da leƙen asiri a fafutukar yaƙi da ta'addanci a Nijar, kamar yadda muka yi a Somalia. Kazalika mun tattauna matakan da za mu ɗauka wajen yaƙi da ta'addanci, wanda shi ne babban abin da ke haifar da rashin zaman lafiya a yankin Sahel," in ji Fidan a hirar da manema labara a Yamai, babban birnin Nijar.
Ministan Tsaron Ƙasa na Turkiyya Yasar Guler, Ministan Makamashi da Albarkatun Ƙasa Alparslan Bayraktar, da Shugaban Hukumar Leƙen Asirin Ƙasa Ibrahim Kalin da sauran manyan jami'an gwamnatin ƙasar suna cikin mahalarta taron manema labaran.
Fidan ya ce Turkiyya tana da ofisoshin jakadanci 44 a cikin ƙasashe 54 na Afirka, yana mai cewa: "Dangantakar da muke da ita da nahiyar Afirka tana samun ci gaba kuma tana ƙara yauƙi a kowace rana. Haɗin-gwiwar da muke da da ƙasashen Afirka a fannin diflomasiyya, tattalin arziki, harkokin kuɗi, tsaro, ilimi da kiwon lafiya na ƙara ƙarfi."
Fidan ya jaddada tarihin alaƙar Turkiyya da Nijar inda ya ce ta samo asali ne tun zamanin Daular Usmaniyya kuma a shekarun baya bayan nan jami'an gwamnatin Turkiyya suna ƙara ƙaimi wajen ƙarfafa wannan dangantaka.
Ya ƙara da cewa, "A yayin da muke ci gaba da yauƙaƙa dangantaka da Afirka, muna kuma aiwatar da wasu tsare da za su mayar da hankali wajen amfana da kuma ci gaban 'yan'uwanmu mutanen karkara. Zaman lafiya da tsaron Afirka na cikin manyan abubuwan da muka sanya a gaba. Kamar yadda aka sani, matsalar rashin tsaro da ta'addanci a yankin Sahel tana ci gaba da yin ƙamari".
Muhimman batutuwa da dama
Fidan ya ce a lokacin da suke ƙasar ta Nijar sun tattauna batutuwa da dama, ciki har da yaƙi da ta’addanci da ilimi da makamashi da lafiya da ciniki da kuma tsaro.
Ya ƙara da cewa a matsayinsu na tawaga, sun tattauna da Firaministan Nijar Ali Lamine Zeine, da ministoci da shugabannin hukumomi.
Sun kuma kafa wata rukunin tattaunawa uku, inda aka yi doguwar tattaunawa sosai kan manufofin kasashen waje da tsaro da makamashi da haƙar ma’adanai da tattalin arziki da cinikayya a cewar Ministan Harkokin Wajen nan Turkiyya.
Fidan ya kuma ƙara da cewa ya samu tarba daga Shugaban gwamnatin Nijar Abdourahamane Tiani, saboda tsaron ƙasa.
Sun yi nazari kan sakamakon tattaunawar da aka yi daban-daban sun kuma amince da ɗaukar wasu matakai, a cewarsa.
'Bibiya sau da ƙafa’
Da yake jaddada manufar Ankara ta bai wa ƙasashen da ake ƙawance da su bayani kan yadda ta tunkari matsalar ta’addanci, Fidan ya bayyana cewa ta’addanci na daga manyan matsalolin da ƙasashen Afirka ke fama da su.
“Mun yi nazari kan yadda za mu bunƙasa ayyuka a ɓangarorin ilimi da kula da lafiya, kamar samar da Asibitin Ƙawance, da shirin tallafin karatu na Maarif,” kamar yadda ya bayyana
“Mun kuma tattauna kan inganta tattaunawa a ɓangarorin tattalin arziki da kuɗaɗe. An tattauna kan batutuwa da dama da kuma ƙarfafa yarjejeniyoyi kan cinikayya.”
Yayin da yake jaddada cewa sun yi tattaunawa mai ma’ana kan batutuwan makamashi da haƙar ma’adanai, Fidan ya ce sun amince su bunƙasa aiki tare da ƙara zuba jari.
“Za mu bibiyi duka matakan da aka ɗauka. Za a aiwatar da abubuwan da aka tare da haɗin kan ma’aikatunmu da abin ya shafa da hukumominmu. Ina fata ziyarar za ta zama mai amfani ga ƙasashen biyu,” a cewarsa.