Rikicin Sudan ya raba miliyoyin mutane da muhallansu sannan ya yi sanadin mutuwar dubban mutane./Hoto:Reuters

Yakin da ya barke a tsakiyar watan Afrilu tsakanin sojojin Sudan da dakarun tsaro na Rapid Response Forces (RSF) ya yi mummunan tasiri musamman a babban birnin Khartoum, kuma ya rikide zuwa rikicin kabilanci a yankin Darfur, sannan ya raba fiye da mutum miliyan uku da muhallansu.

Ga wasu muhimman bayanai game da yakin a yayin da a yau ake cika kwana 100 da soma shi:

15 ga watan Afrilu - Bayan an kwashe makonni ana zaman dar-dar game da shirin mayar da mulki hannun gwamnatin farar-hula, mummunan rikici ya barke a Khartoum sannan an bayar da rahotannin yin kananan rikice-rikice a wasu biranen kasar

Dakarun RSF wadanda ke biyayya ga mataimakin shugaban kasa Mohamed Hamdan Dagalo, da aka fi sani da Hemedti, sun far wa gidan shugaban kasa Janar Abdel Fattah Al-Burhan, a yayin da suka yi yunkurin kwace muhimman wurare a babban birni kasar.

16 ga watan Afrilu - Majalisar Dinkin Duniya (MDD) da Hukumar Bayar da Abinci ta WFP sun bayyana dakatar da ayyukansu na dan wani lokaci a Sudan, kuma wannan shi ne daya daga cikin ayyyukansu mafi girma a duniya.

Sun dauki mataki ne bayan an kashe uku daga cikin ma'aikatansu na bayar da agaji a wani hari da aka kai musu da sanyin safiya. WFP ya ce zai koma aiki ranar 1 ga watan Mayu, bayan ya yi gargadin cewa fiye da mutum miliyan uku suna cikin barazanar fuskantar yunwa kuma zai yi wahala manoma su iya yin noma a lokacin

21 ga watan Afrilu - Adadin mutanen da ke tserewa sakamakon rikicin da ake yi a Khartoum ya yi matukar karuwa bayan da aka ci gaba da luguden wuta da sace-sace da arangama tsakanin sojin Sudan da dakarun RSF a sassa daban-daban na birnin. Mutane da dama sun nemi mafaka a wajen Khartoum sannan wasu sun nufi iyakokin Sudan don tsallakawa zuwa wasu kasashe.

22 ga watan Afrilu- Amurka ta sanar cewa dakarunta na musamman sun kwashe dukkan ma'aikatan ofishin jakadancinta da ke Khartoum. Turkiyya, Faransa, Nijeriya, Birtaniya da sauran kasashe su ma sun bi sahun Amurka wurin kwashe 'yan kasashensu, abin da ya aka bar Sudan domin kula da kanta.

25 ga watan Afrilu - Ahmed Haroun, tsohon ministan kasar da Kotun Hukunta Masu Manyan Laifuka ta Duniya, ICC take nema kan zarge-zargen aikata laifukan yaki a Darfur, ya ce shi da wasu tsoffin jami'an tsohuwar gwamnatin Omar al-Bashir sun fice daga kurkukun kasar.

Daga bisani jami'ai suka tabbatar cewa an sauya wa al-Bashir, wanda shi ma Kotun Hukunta Masu Manyan Laifuka ta Duniya take nema, matsuguni zuwa asibiti soji kafin ma a soma rikicin.

5 ga watan Mayu - Asusun Kua da Yara na Majalisar Dinkin Duniya UNICEF ya ce an sace allurar rigakafi fiye da miliyan daya ta citar shan-inna, yana mai gargadin cewa akwai yiwuwar rugujewar fannin kiwon lafiya sakamakon yakin. Kazalika WFP ya bayar da rahoton cewa ana yin gagarumar sata ta kayayyakin da ya kai kasar.

20 ga watan Mayu- Yayin taron da Saudiyya da Amurka suka hada a Jeddah don magance rikicin, bangarori biyu da ke fada da juna a Sudan sun yi alkawarin tsagaita wuta ta kwana bakwai da zummar bari a kai kayan agaji ga mabukata. Sai dai daga bisani an bayar da rahoton cewa sun ki cika wannan alkawari, lamarin da ya sa masu kai agajin gaggawa suka rika fuskantar matsaloli. An dage tattaunawar ta Jeddah zuwa watan Yuni.

29 ga watan Mayu - Shugaban hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ya ce akwai gyara a kiyasin da aka yi cewa kimanin mutum miliyan daya ne za su tsere daga Sudan daga wancan lokacin zuwa watan Oktoba domin kuwa lamarin ya munana, yana mai gargadin cewa safarar makamai da ta mutane za ta watsu zuwa kasshen da ke yankin wanda da ma yana fama da rashin tsaro.

8 ga watan Yuni - Shigar dakarun 'yan tawayen SPLM-N da ke Kudancin Kordofan cikin rikicin ya sanya fargabar cewa yakin zai bazu zuwa kudancin Sudan. Rikicin da aka rika yi a jihar Kudancin Kordofan da Blue Nile ya sa mutane sun rika tserewa daga yankunan.

14 ga watan Yuni - An kashe gwamnan Yammacin Darfur Khamis Abbakar awanni bayan ya yi hira da wani gidan talbijin inda ya zargi dakarun RSF da abokansu da aiwatar da kisan kare-dangi kan kabilun da ba Larabawa ba ne.

Dubban farar-hula sun yi yunkurin tserewa ta kafa zuwa Chadi bayan kisansa amma an rika kai musu hari.

19 ga watan Yuni- Masu bayar da agaji na duniya sun yi alkawarin bai wa Sudan da makwabtanta tallafin $1.5 a wani taro da suka yi a Geneva, inda suka ce ana bukatar yin amfani da kusan rabin kudin don ayyukan jinkai.

13 ga watan Yuli - Masar ta soma sabuwar tattaunawar shiga tsakani don wanzar da zaman lafiya tsakanin bangarorin da ke rikici a Sudan a wani taro da aka gudanar a birnin Alkahira. Shugaban kasar Ethiopia ya ce ya kamata kungiyar kasashen Gabashin Afirka ta IGAD ta jagoranci wannan yunkuri, sai dai an yi ta nuna fargaba bayan da Sudan ta yi watsi da kiran nasa.

14 ga watan Yuli - Kungiyar Sudan Conflict Observatory da ke bin diddigin rikicin Sudan ta fitar da rahoton da ke zargin dakarun RSF da abokansu da lalata garuruwa akalla 26 a yankin Darfur. Kwana guda kafin fitar da rahoton, Kotun ICC ta ce tana gudanar da bincike kan abin da ya faru a Darfur. Sai da dakarun RSF sun ce rikicin yankin na kabilanci ne.

Reuters