Manjo Janar Abdou Sidikou Issa ya samu horo a bangarori daban-daban na soji a ciki da wajen Jamhuriyyar Nijar. Photo/actuniger

Daga Mustapha Musa Kaita

A ranar Juma’a ne Shugaban Jamhuriyar Nijar Mohamed Bazoum ya sauya shugaban sojojin kasar wanda ya shafe sama da shekara uku yana jagoranci.

Shugaba Bazoum ya cire Janar Salifou Mody daga kan mukaminsa kuma ya maye gurbinsa da Manjo Janar Abdou Sidikou Issa.

A hukumance dai gwamnatin kasar ba ta bayyana dalilin yin wannan garambawul din ba. Hasalima sai da aka kara wa Janar Salifou Mody girma zuwa cikakken janar din soja kafin a sauke shi daga mukaminsa.

Janar Mody ya jagoranci rundunar sojin Nijar ne a lokacin da hukumomin kasar ke bayyana irin nasarorin da suka samu a cigaba da fafatawa da mayakan da suka addabi kasar.

Hakan ne ya sa masu sharhi ke ganin an yi rabuwar arziki tsakanin gwamnati da Janar din.

“Da wani laifi ya yi, babu yadda za a yi a kara mashi girma— sai da ya zama cikakken janar sa’annan aka sauke shi, don haka a nawa hasashen sauya shi da aka yi, wani aiki za a ba shi,” in ji Farfesa Addo Mahamane, malamin tarihi a Jami’ar Abdou Moumouni ta birnin Yamai.

Ya kara da cewa duk wanda aka yi wa irin wannan, alama ce ta karamci da kuma yabo a gare shi.

Janar Salifou ya bayar da gudunmawa wurin yakar masu ikirarin jihadi a yankin sahel. Photo/actuniger

‘Sharar Fagge’

Shi ma Alkassoum Abdourahmane na cibiyar Sahel International Solidarity Forum, da ke sharhi kan tsaro, ya ce Janar Salifou Mody ya taka rawar gani matuka wurin tabbatar da tsaro a Jamhuriyar Nijar da yankin Sahel duk da kalubalen tsaro da kasar ke fuskanta daga makwabtanta kamar Nijeriya da Burkina Faso da Mali.

Ya ce cikin irin jajircewar da Janar Mody ya nuna har da kokarin da ya rinka yi na shiga dazukan da ke Mali da kuma Nijeriya domin fatattakar masu tayar da kayar baya.

Haka kuma ya bayyana cewa irin ayyukan da Janar Mody ya yi, kamar sharar fagge ce ga wanda ya gaje shi domin sai dai ya dora a kansu.

“Irin tsarin da shi wannan wanda ya tafi ya shimfida bisa maganar ayyuka da fasahohi, gaskiya duk wanda aka dauko aka kawo ya kamata ya ci gaba da tafiyar da wannan tsarin,” in ji shi.

‘Kalubale’

Masana na ganin babban kalubalen da sabon shugaban rundunar sojin zai fuskanta shi ne shawo kan matsalar masu tayar da kayar baya a kasashen da ke makwabtaka da Nijar.

A cewar Alkassoum Abdourahmane, duk da ana samun ci gaba wajen murkushe ‘yan bindiga ta bangaren iyakar Nijeriya da Mali da Burkina Faso, amma akwai wasu wurare da ya kamata a kara mayar da hankali a kansu.

“Inda rauni yake har yanzu shi ne yankin iyaka da arewa maso yammacin Nijeriya ta wajen Madarumfa domin kuwa har yanzu ana zuwa ana daukar mutane da sauransu,” in ji Alkassoum.

Ya ce akwai yiwuwar Manjo Abdou zai samu nasara ganin cewa ya rike mukamai da dama na soji da kuma irin horon da ya samu daban-daban.

Farfesa Addo Mahamane ya bayyana cewa an samu ci gaba matuka a kasar ta fuskar tsaro yana mai cewa a duk shekara ana daukar dubban jami’an tsaro kuma ana sayen makamai wadanda jami’an za su yi amfani da su.

“Har Turkiyya sai da shugaban kasarmu ya je ya sayo makamai na yaki domin fatattakar masu tayar da mayar baya,” in ji Addo Mahamane.

TRT Afrika da abokan hulda