Mamakon ruwan sama da amabaliyar da aka shafe tsawon mako uku ana yi a Nijar sun yi sanadin mutuwar mutum 21, lamarin da ya shafi kusan mutum 6,000, a cewar alkaluman Ma'aikatar Harkokin Cikin Gida a ranar Alhamis.
Ma'aikatar ta ce mutum takwas sun nutse a ruwa sannan wasu 13 sun mutu a cikin gidajen da mamakon ruwan ya rushe su.
Wasu mutum 26 din sun jikkata sannan kusan dabbobi 4,000 sun mutu ko sun ɓata, a cewar jami'ai a jawabin da suka yi a gidan talabijin na ƙasar.
Tun shiga daminar bana yankin Maradin ne mummunan yanayin ambaliyar ya fi shafa, inda jami'ai suka ce mutum 14 ne suka rasu a can.
Yawanci dai a kan fara damina ne daga watan Yuni har Satumba a ƙasar ta Yammacin Afirka.
A shekarar 2022 kusan mutum 195 ne suka mutu kuma lamarin ya shafi mutum 400,000, waɗanda da yawansu suka rasa gidajensu.