Gwamnatin mulkin soji ta Mali ta dakatar da gidan talbijin na Faransa LCI daga aiki a ƙasar tsawon watanni biyu, inda ta zarge shi da yin "zarge-zarge na ƙarya " game da rundunar sojin ƙasar da abokansu na Rasha.
"An dakatar da gidan talbijin na LCI television daga watsa labarai na rediyo da talbijin a Mali tsawon watanni biyu" daga ranar 23 ga watan Agusta, a cewar hukumar da ke sanya ido kan kafafen watsa labarai ta Mali a wata sanarwa da ta fitar ranar Asabar.
Tun bayan da sojoji suka yin juyin mulki a Mali a 2020 da 2021, suke yaƙi da ƙungiyoyin masu tayar da ƙayar baya da masu neman ɓallewa daga ƙasar da ke da ƙarfi a arewacin Mali.
Sojojin sun kori Faransa daga ƙasar, sannan suka ƙarfafa alaƙa da ƙasar Rasha, inda sojojin haya na Wagner suke taimaka musu wajen yaƙi da 'yan ta'adda.
A ƙarshen watan Yuli, 'yan tawaye Abzinawa sun yi wa sojojin Mali da sojojin haya na Rasha kwanton-ɓauna a arewacin ƙasar, inda suka yi iƙirarin kashe mayaƙa 84 na Wagner da sojojin Mali Mali.
A cewar hukumar da ke sanya ido kan kafofin watsa labarai, wani mai sharhi a gidan talbijin na LCI ya yi zarge-zarge masu cike da ƙarya a wani shiri da ake kira "Wagner Decimated in Mali: the Hand of Kyiv".
Hukumar ta ce shirin na ƙunshe da "kalamai na cin zarafi da ƙarairayi game da rundunar sojojin Mali da abokan haɗin-gwiwarta na Rasha".
Ranar 4 ga watan Agusta ne ta yanke hulɗa da Ukraine kan zargin goyon bayan 'yan ta'adda a ƙasar, zargin da mahukunta a Kyiv suka musanta.
Tun bayan da sojoji suka yi juyin mulki sau biyu a Mali, sun riƙa dakatar da kafofin watsa labaran ƙasashen waje.
Sun dakatar da fitattun kafofin watsa labaran Faransa irin su RFI da France 24 a watan Afrilun 2022, da kuma France 2 a farkon shekarar 2024.
Kazalika ƙasashen Burkina Faso da Nijar, waɗanda su ma suke ƙarƙashin mulkin soji suna matsa lamba kan kafofin watsa labarai.
Burkina Faso ta dakatar da LCI a watan Yunin 2023 bayan wani wakilinta ya bayar da rahotanni game da yanayin tsaron ƙasar, waɗanɗa sojoji suka ƙaryata.