Malawi ta karbi rigakafin cutar kwalara miliyan 1.4 daga kungiyar agaji ta International Coordinating Group ICG da kuma kungiyar Vaccine Alliance a daidai lokacin da kasar ke fuskanar barazanar bazuwar kwalara.
Wannan na zuwa ne sakamakon illar da mahaukaciyar guguwa ta Tropical Cyclone Freddy da ta afka wa gundumomi 15 a Kudancin Malawi a farkon watan Maris ta yi.
Kusan mutum miliyan biyu wannan guguwa ta yi wa barna, sa’annan sama da mutum dubu 600 ta raba da muhallansu.
Sakamakon hanyoyin ruwa da cutar ta lalata, mazauna wuraren na cikin barazanar kamuwa da cututtuka musamman wadanda ake dauka ta ruwa kamar kwalara.
“Irin illolin da Cyclone Freddy ta yi kan kiwon lafiya da kuma hanyoyin ruwa da tsafta za su iya yin barazana ga ci gaban da aka samu na takaita barkewar cutar kwalara a Malawi ganin irin koma bayan da aka samu a ‘yan makonnin nan,” in ji Dakta Dr Neema Rusibamayila Kimambo, wakiliyar WHO a Malawi.
“Sakamon hadin gwiwar da WHO da UNICEF da sauran abokan hulda suka yi, muna taimaka wa ma’aikatar lafiya domin kare ci gaban da muka samu domin dakile barkewar cutar kwalara ta amfani da rigakafin OCV.”
Kasar Malawi dai na fama da barkewar cutar kwalara mafi muni a tarihin kasar. Cutar ta barke tun a watan Maris din 2022 inda aka samu mutum 57,656 da suka kamu da cutar sannan mutum 1,736 suka rasu a zuwa 13 ga watan Afrilun 2023.
Mece ce Kwalara?
Cutar kwalara ko kuma amai da gudawa cuta ce da take iya kashe mutum cikin sa’o’i bayan kamuwa da ita.
Har yanzu kwalara babbar barazana ce ga lafiyar al’umma, inda ake samun mutum miliyan 1.3 zuwa miliyan hudu da ke kamuwa da cutar a duk shekara, kamar yadda hukumar CDC ta bayyana.
Haka kuma hukumar ta bayyana cewa ana samun tsakanin mutum 21,000 zuwa 143,000 da ke mutuwa sakamakon wannan cuta a duk shekara.
A 2018, an samu barkewar kwalara a Kamaru inda mutum 237 suka kamu da cutar sannan 17 suka rasa rayukansu.
Haka kuma a Habasha a 2019, mutum 525 aka tabbatar sun kamu da cutar sa’annan 16 suka rasu, kamar yadda CDC ta bayyana. Hukumar Lafiya ta Duniya ta bayyana tsafta a matsayin wani ginshiki na yaki da cutar kwalara.
Ta ce akwai bukatar a sha ruwa mai tsafta da kuma cin abinci mai tsafta.
Haka kuma ta ce akwai bukatar a rinka wanke hannu da sabulu idan an yi bayan gida da duk lokacin da mutum zai ci wani abinci.