Masu walda na amfani da sinadarin na carbide wurin aikinsu./Hoto:Reuters

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta Nijeriya NAFDAC ta yi gargadi kan shan ‘ya’yan itatuwan da aka nuka da sinadarin carbide.

Shugabar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta yi gargadin a Abuja ranar Talata yayin taron wayar da kan jama'a game da illolin sayar da magunguna a kan titi da kuma sha ko cin ‘ya’yan itatuwa da aka nuka da carbide.

Ta ce sha ko cin ‘ya’yan itatuwan da aka nuka da wannan sinadarin kan iya jawo cutar daji da ciwon zuciya da koda da hanta.

Ta bayyana cewa abu ne mai kyau nuka ‘ya’yan itatuwa amma nuka su da wannan sinadarin na da matukar illa ga lafiya.

'Yan Nijeriya sun sha kokawa kan yadda masu sayar da kayan marmari kamar su mangwaro da lemo da ayaba da gwanda da sauransu suke amfani da sinadarin.

Mene ne sinadarin carbide?

Calcium carbide wani sinadari ne kamar hoda kuma yana wari kamar tafarnuwa. A wani lokacin za a gan shi a dunkule kamar kanwa.

Ana amfani da shi ne galibi domin wurin sarrafa karfe yayin da kuma masu walda ke amfani da shi wurin gudanar da aikinsu.

Asalin sinadarin ana hada shi ne ta hanyar amfani da sinadarin Calcium hydroxide da sinadarin coke.

Illolin sinadarin carbide a abinci

Hukumar NAFDAC ta tabbatar da cewa sinadarin carbide na da illa matuka a abinci domin kuwa yana iya jawo cutar kansa wato ciwon daji.

Sinadarin yana daga cikin sinadaren da aka yi itifaki suna da hatsari saboda yana dauke da wasu sinadarai da suka hada da arsenic da phosphine masu mugun hatsari.

Wani bincike da ma’aikatar lafiya ta Jihar New Jersey ta Amurka ta yi ya nuna cewa:

- Calcium carbide zai iya yi wa mutum illa idan ya shake shi ta hanci.

- Zai iya jawo matsala ga fatar dan adam ko jawo kuraje ko idan ya taba jiki.

- Illa ga ido idan sinadarin ya shiga ciki, haka kuma zai iya jawo ciwo a baki da hanci da makogoro.

- Shakarsa zai iya kawo matsala ga huhu, idan kuma aka shake shi da yawa zai sa ruwa ya taru a huhu abin da ka iya zai jawo wata babbar matsala.

Ta ya za a iya gane ‘ya’yan itatuwan da aka nuka da carbide?

Hukumar NAFDAC ta sha wayar da kan jama'a hanyoyi masu inganci na nuka kayan marmari.

Kazalika tana jan hankalin jama'a kan yadda za su gano kayan marmarin da aka nuka da carbide.

Hukumar ta ce akasarin ‘ya’yan itatuwa irin su mangwaro da ayaba da lemo, daga waje za a ga sun yi dorawa sun nuna lafiya lau, amma idan mutum ya bude cikin zai ji da tauri ba su gama nuna ba.

Haka kuma launin ‘ya’yan itatuwan nunarsu yakan bambanta inda misali a jikin mangwaro za a ga wani sashe ya nuna wani kuma bai nuna ba.

TRT Afrika