Kasar Indonesia ta bai wa Nijeriya tallafin rigakafin Pentavalent 1,580,000 wadda ake yi wa yara.
Babban daraktan hukumar kiwon lafiya a matakin farko na Nijeriya Faisal Shuaib ne ya tabbatar da hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Twitter inda ya ce rigakafin za su matukar taimakawa wurin cike gibin da ake da shi na rigakafi a kasar da kuma bai wa kowane yaro samun damar amfana da rigakafin.
Rigakafin ta Pentavalent dai na kare yara daga cututtuka da suka hada da ciwon hanta da diphtheria da tetanus da wasu cututtukan.
“Muna matukar godiya ga gwamnatin Indonesia kan irin wannan taimako, wannan wata shaida ce ta hadin kanmu wurin samar da lafiya a duniya.
Wannan tallafin zai ceci rayuka ba adadi da kuma tuna mana da karfin hadin kan duniya,” in ji Faisal Shuaib.
Gwamnatin ta ce za ta fi mayar da hankali wurin rarraba rigakafin musamman ga yaran da ke cikin barazanar kamuwa da cututtuka da kauyuka da wuraren da ba su da isassun asibitoci.
Hukumar da ke kula da cututtuka masu yaduwa ta Nijeriya NCDC ta sha kokawa kan karancin yi wa yara rigakafi.
Ko a kwanakin baya sai da ta koka kan cewa karancin yin rigakafin ne ya ja barkewar cutar makoshi ta diphtheria wadda rigakafin Pentavalent da Indonesiya ta bai wa Nijeriya tallafinta ke taimakawa wurin kiyaye kamuwa da cutar.