'Yan majalisar  dokokin sun yi wa kasafin kudin, wanda Shugaba ya bayyana  a matsayin "Budget of Renewed Hope" wato "Kasafin Sabunta Fata", kwaskwarima./Hoto:Ofishin shugaban Nijeriya

Majalisun dokokin Nijeriya - Majalisar Dattawa da ta Wakilai - sun amince da naira tiriliyan 28.77 a matsayin kasafin kudin 2024 ranar Asabar, bayan sun kara yawan kudin da kasar za ta kashe a shekarar.

'Yan majalisun dokokin sun kara Naira tiriliyan 1.2 a kan naira tiriliyan 27.5 da shugaban kasar Bola Tinubu ya gabatar musu ranar 29 ga watan Nuwamba.

Sun yi karin ne sakamakon korafin da ma'aikatun gwamnati suka yi na rashin isassun kudi a kasafin da shugaban kasar ya gabatar da kuma bukatar da shugaban ya mika musu ta kara yawan kasafin kudi saboda yadda darajar naira ke ci gaba da raguwa.

Kasafin kudin da aka yi wa kwaskwarima a takaice:

  • Jumullar kasafin kudin 2024 - Naira tiriliyan 28.77
  • Manyan ayyuka - Naira tiriliyan 8.7
  • Ayyukan yau da kullum - Naira tiriliyan 9.99
  • Biyan Bashi - Naira tiriliyan 8.27
  • Sauyin dala - Kasafin ya dogara ne a kan sauya duk dala daya a kan Naira 800.

Tinubu ya ce zai mayar da hankali a kan harkokin tsaro da noma da sufuri, da kiwon lafiya, da dai sauran muhimman sassa, a kasafin kudin, wanda shi ne na farko da ya gabatar a matsayin shugaban kasa.

TRT Afrika