Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya saka takunkumi kan wasu janar ɗin soji biyu na rundunar RSF ta Sudan bisa rawar da suka taka wurin yaƙi da sojojin ƙasar, lamarin da ya jawo aka aikata ta'asa a ƙasar.
Sudan ta faɗa cikin rikici a tsakiyar Afrilun 2023, bayan da fargabar da ta jima tsakanin sojojin ƙasar da kuma rundunar RSF ta rikiɗe ta koma yaƙi a Khartoum babban birnin ƙasar, inda bayan haka yaƙin ya rinƙa bazuwa zuwa wasu sassa na ƙasar.
Majalisar Ɗinkin Duniya ta ce sama da mutum 14,000 aka kashe, an kuma jikkata 33,000 kuma a baya-bayan nan majalisar ta yi gargaɗin cewa Sudan ɗin na dab da faɗawa cikin halin matsananciyar yunwa.
Kwamitin da ya saka takunkumin ya ƙara da sunayen wasu janarori a cikin jerin takunkumin waɗanda suka haɗa da Manjo Janar Osman Mohamed Hamid Mohamed, wanda shi ne shugaban ayyuka na rundunar ta RSF da kuma Manjo Janar Abdel Rahman Juma Barkalla wanda shi ne kwamandan RSF a Yammacin Darfur.
Ofishin Jakadancin Majalisar Dinkin Duniya na Biritaniya ya wallafa a shafinsa na X cewa an kara hafsoshin biyu ne saboda barazana ga zaman lafiya, tsaro da zaman lafiyar Sudan, "da suka hada da tashe-tashen hankula da take hakin bil'adama."
Ƙwace iko da kadarori
Takunkumin na Majalisar Dinkin Duniya ya umarci dukkan kasashe da su ƙwace iko da kadarorin janarorin tare da sanya dokar hana zirga-zirga a kansu. Baitul malin Amurka ya sanya takunkumi kan manyan hafsoshin biyu a farkon shekarar nan, tare da ƙwace iko da duk wata kadararsu da ke Amurka tare da haramta duk wata hada-hadar kudi da su.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta bayyana a cikin wani rahoto da ta fitar a watan Mayu cewa hare-haren da dakarun sa kai na RSF da kawayansu suka kai, wanda ya yi sanadiyar mutuwar dubban mutane a Darfur a shekarar 2023, ya zama wani shiri na kisan ƙare dangi na ƙabilanci ga mutanen da ba Larabawa ba.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta ce RSF da mayakanta sun kai hari kan kabilar Masalit da wasu kungiyoyin da ba na Larabawa ba a El Geneina, babban birnin jihar Darfur ta Yamma.
Kungiyar kare hakkin bil adama ta Human Rights Watch ta ce an azabtar da 'yan Masalit da aka kama, an kuma yi wa mata da 'yan mata fyade tare sace kayayyaki a unguwanni da lalata su.
Kungiyar ta RSF ce ke rike da manyan biranen jihohi hudu daga cikin biyar na Darfur.