A sanarwar da majalisar ta fitar a ranar Talata, ta ce wannan dokar tana cikin dokar masarautu ta 2024. Hoto: Kano Assembly

Majalisar Dokokin Jihar Kano ta ce ta amince da dokar kirkirar masarautu masu daraja ta biyu ga masarautu uku da suka haɗa Rano da Gaya da Karaye.

A sanarwar da majalisar ta fitar a ranar Talata, ta ce wannan dokar tana cikin dokar masarautu ta 2024.

Hakan na zuwa ne a lokacin da ake ci gaba da tirka-tirka kan dokar da gwamnatin jihar ta sanya wa hannu ta rushe masarautu hudu na Gaya da Rano da Karaye da kuma Bichi, da sauke Sarki Aminu Ado Bayero da kuma mayar da Sarki Muhammadu Sanusi na II.

A yayin da yake gabatar da ƙudurin dokar, mataimakin shugaban majalisar Mohd Bello Butu Butu ya ce ƙirƙirar masarautu masu daraja ta biyu zai inganta al’adu da al’amuran addinin Musulunci da magance rikice-rikice a tsakanin al’ummomin yankunan.

Da yake ƙarin haske kan kudirin, shugaban masu rinjaye na majalisar, dan majalisar mai wakiltar mazabar Dala Lawan Hussain Chediyar ‘Yan Gurasa ya ce doka ta bai wa gwamna ikon nada wanda ya cancanta a matsayin sarki mai daraja ta biyu na kowace masarauta wanda zai kasance karkashin Sarkin Kano mai daraja ta daya.

Dokar ta hada da masarautar Rano wacce kananan hukumomin Rano da Bunkure da Kibiya ke ƙarƙashinta, sai Masarautar Gaya wadda ta kunshi kananan hukumomin Gaya da Ajingi da Albasu, sai kuma Masarautar Karaye da ta hada da kananan hukumomin Karaye da Rogo.

Kakakin majalisar Alh. Jibril Ismail Falgore ne ya jagoranci zaman. Kuma a yanzu da zarar Gwamna abba Kabir Yusuf ya amince da kudurin, to zai zama doka nan take.

TRT Afrika