Ƴan majalisun dokokin Birtaniya sun amince da ƙudurin dokar da zai sa a kai masu neman mafaka da ƴan ci-rani na ƙasar zuwa Rwanda bayan an yi zazzafar muhawara.
Mambobin babbar majalisar dokokin Birtaniya waɗanda ba zaɓensu aka yi, sun yi garambawun sosai a cikin ƙudurin dokar sannan suka aika da shi gaban ƴan majalisar dokokin da aka zaɓa, waɗanda suka amince da shi ranar Talata inda yanzu zai zama doka.
Firaiministan Birtaniya Rishi Sunak ya yi alƙawarin soma aika wa da masu neman mafaka a ƙasar zuwa Rwanda nan da mako 10 zuwa 12.
Sunak ya ce gwamnatinsa ta ɗauki hayar jiragen sama da ƙwararrun ma'aikata da za su kai ƴan ci-rani Rwanda, a wani mataki da yake fata zai ƙara wa jam'iyyarsa ta Conservative tagomashi kafin zaɓen da za a yi nan gaba a wannan shekarar.
A baya Majalisar Dattawan ƙasar ta ƙi amince da ƙudurin ba tare da yin wasu sauye-sauye ba, amma daga bisani ta yarda da shi bayan Sunak ya ce gwamnatinsa za ta tilasta wa Majalisar Dokoki zama ranar Litinin don amincewa da ƙudurin.
"Babu abin da zai hana jirage tafiya Rwanda," kamar yadda Sunak ya shaida wa manema labarai ranar Litinin.