Majalisar Dattijan Zimbabwe ta amince da wani kudirin doka na soke hukuncin kisa, wani muhimmin mataki na yin watsi da dokar da aka yi amfani da ita a kasar da ke kudancin Afirka kusan shekaru 20 da suka gabata.
Majalisar ta fada a ranar Alhamis cewa, ‘yan majalisar dattawan kasar ne suka amince da kudirin ranar Laraba da daddare.
Za a soke hukuncin kisa idan shugaban kasar ya sanya wa dokar hannu, abin da ake kyautata zaton zai yi hakan.
Ƙasar ta Kudancin Afirka tana amfani da rataya, kuma hukuncin kisa na ƙarshe da ta zartar shi ne kashe wani mutum a shekarar 2005, daga cikin dalilan rashin aiwatar da kisan shi ne babu wanda aka samu don ɗauka aikin mai aiwatar da hukuncin kisa, ko mai ratayewa.
Fiye da fursunoni 60 ne ke jiran a awitar musu da hukuncin kisa
Tun a shekara ta 2017 Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya fito fili ya bayyana adawarsa da hukuncin kisa.
Ya bayar da misali da kansa inda aka yanke masa hukuncin kisa - wanda daga baya aka sauya shi zuwa daurin shekaru 10 a gidan yari - saboda tarwatsa jirgin kasa a lokacin yakin neman 'yancin kai a kasar a shekarun 1960.
Ya yi amfani da afuwar da shugaban kasa ke iya yi wajen sassauta hukuncin kisa zuwa daurin rai-da-rai.
Kungiyar kare hakkin dan adam ta Amnesty International, wacce ke adawa da hukuncin kisa, ta bukaci Mnangagwa ya sanya hannu kan kudirin dokar "ba tare da bata lokaci ba" tare da sassauta hukuncin kisa. Kasar Zimbabwe na da fursunoni sama da 60 a halin yanzu da ake yanke musu hukuncin kisa.
A cewar Amnesty, kusan kashi uku bisa hudu na kasashen duniya ba sa aiwatar da hukuncin kisa.
Zimbabwe na daya daga cikin fiye da kasashe goma sha biyu a Afirka kuma sama da 50 a fadin duniya da ke da hukuncin kisa da aka sanya a cikin doka ba tare da dakatar da shi a hukumance ba.
Amnesty International ta ce ta samu kisa 1,153 da aka sani a duniya a shekarar 2023, sama da 883 a shekarar da ta gabata, duk da cewa kasashen da suka aiwatar da hukuncin kisa sun ragu daga 20 zuwa 16. Hakan kuwa ya faru ne Saboda aiwatar da hukuncin a sirri, alkalumman ba su hada da na Koriya ta Arewa da Vietnam da kuma China ba.
Kasar China ce kan gaba wajen aiwatar da hukuncin kisa a duniya, inda ake kyautata zaton an kashe dubban mutane, in ji Amnesty a wani rahoto da ta fitar a watan Oktoba.
'Matakai masu kyau'
A Iran da Saudi Arabiya aka aiwatar da kusan kashi 90% na duk hukuncin kisa da Amnesty ta tattara a shekarar 2023.
Amurka ta samu karuwar hukuncin kisa daga 18 a shekarar 2022 zuwa 24 a shekarar 2023. A shekarar da ta gabata, China da Iran da Saudi Arabia da Somalia da Amurka sun fi aiwatar da hukuncin kisa.
Amnesty ta ce Zimbabwe na cikin kasashe hudu na Afirka tare da Kenya da Laberiya da Ghana da suka dauki "matakai masu kyau" kwanan nan don soke hukuncin kisa.