Majalisar dattawan Kenya ta kaɗa ƙuri'ar amincewa da tsige Mataimakin Shugaban Ƙasar Rigathi Gachagua.
An tuhumi Gachagua da laifuka 11, kuma Majalisar Dattawan Kenya mai wakilai 67 ta buƙaci a tabbatar da akalla daya daga cikin dalilan na tsige shi.
Zarge-zarge 5 da suka hada da saɓa wa kundin tsarin mulkin Kenya da kuma rashin ɗa'a, sun samu ƙuri'u kashi biyu bisa uku na ƙuri'u (ƙuri'u 45 na "e") a ranar Alhamis, lamarin da ke tabbatar da korar Gachagua.
Sanatocin Kenya 54 sun amince da tuhumar da ake yi wa mataimakin shugaban kasar cewa ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Kenya.
Gachagua ya sha alwashin ɗaukar matakin kai ƙara kotu
Akalla kashi biyu bisa uku na 'yan majalisar dattawa 67 - wato 45 - na bukatar kaɗa ƙuri'ar "e" kan duk wasu tuhume-tuhumen da ake yi na tsige Gachagua.
Bisa kundin tsarin mulkin kasar Kenya, mataimakin shugaban kasa ya daina riƙe muƙaminsa bayan da majalisar dokokin kasar da kuma majalisar dattawa suka tsige shi.
A baya Gachagua ya sha alwashin kalubalantar tsige shi daga mukaminsa ta hanyar shigar da ƙara kotu, yana mai cewa shigar jama'a cikin tuhume-tuhumen da ake yi masa na tsige shi bai dace ba.
Mataimakin shugaban kasar ya fuskanci tuhume-tuhume 11 da suka hada da almundahana da ta kai yawan kudin Kenya shilling biliyan 5.2 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 40.3 a cikin shekaru biyu na farko na mulki.
Zargin cin hanci da rashawa
Gachagua, wanda ya musanta zargin, ta bakin lauyoyinsa ya ce zargin da ake yi masa ba shi da wata hujja.
Dan Majalisar Kibwezi ta Yamma (MP) Mwengi Mutuse, wanda shi ne ya gabatar da ƙudirin tsige Gachagua a Majalisar Dokokin Ƙasar, ya ce a cikin shekaru biyu da suka wuce, mataimakin shugaban kasar ya karbi albashin shillings miliyan 24, kwatankwacin dala 186,000.
Mutuse ya ƙara da cewa, a gabanin zaben shugaban kasa na watan Agustan 2022, Gachagua ya ayyana dukiyarsa a matsayin shilling miliyan 800, kwatankwacin dala miliyan 6.8.
A cewar Mutuse, arzikin Gachagua ya yi ƙaruwar da ta dasa zari a cikin shekaru biyu da suka wuce, wanda ke nuna cewa an samu ƙaruwar dukiyar ne ta hanyar cin hanci da rashawa.
Dukiya 'daga dan uwa'
An kuma zargi Mataimakin Shugaba Gachagua mai shekaru 59 da yin zagon ƙasa ga gwamnati, da kuma shiga harkokin siyasar kabilanci.
Gachagua ya yi watsi da zarge-zargen da aka yi masa, yana mai bayyana su da "ƙarya ta son zuciya."
Mataimakin shugaban kasar ya ce dukiyarsa ta fito ne daga sana’o’insa daban-daban da suka haɗa da kiwo, da kuma dukiyar da ya gada daga ɗan'uwansa marigayi NDERITU Gachagua.
Matakin na Majalisar Dattijan ya zo ne mako guda bayan da majalisar ta tsige mataimakin shugaban kasa kan wannan batu.
An zaɓe shi tare da Shugaba William Ruto
A ranar 8 ga watan Oktoba ‘yan majalisar wakilai 282 ne suka kada ƙuri’ar amincewa da tsige shi, yayin da 44 suka ƙi amincewa da shi, kuma mamba daya ya ƙi kaɗa ƙuri’a.
An zaɓi Gachagua ne tare da Shugaba William Ruto a zaɓen shugaban ƙasar Kenya da aka gudanar ranar 9 ga watan Agustan 2022.
Kafi sannan, ya taɓa zama dan majalisa na farko a mazabar Mathira ta Tsakiyar Kenya, tun daga 2017.