Shugabannin Afirka a ranar Asabar sun zabi Ministan Harkokin Wajen Djibouti a matsayin wanda zai jagoranci hukumar Ƙungiyar Tarayyar Afrika.
Mahmoud Ali Youssouf ya doke Raila Odinga tsohon Firaministan Kenya da Richard Randriamandrato, tsohon Ministan Harkokin Wajen Madagascar a kuri'ar da aka kaɗa a taron na AU da aka gudanar a Addis Ababa, babban birnin kasar Habasha.
AU tana da kasashe 55 mambobi. Shugabannin ƙasashen nahiyar ne ke zaɓen shugaban hukumar, wanda shi ne babban jami'in zartarwa na sakatariyar hukumar da ke birnin Addis Ababa da ke jagorantar kungiyar ta AU.
Youssouf, wanda zai yi wa'adi na shekaru huɗu, ya maye gurbin Moussa Faki na Chadi, wanda ke rike da mukamin tun shekarar 2017.
Youssouf ya kasance ministan harkokin wajen Djibouti tun shekara ta 2005.
A matsayinsa na sabon shugaban hukumar ƙungiyar ta AU, Youssouf ya gaji ƙalubale daban-daban da suka haɗa da ƙaruwar mulkin soji a ƙasashen Yammacin Afirka da kuma rikicin ‘yan tawaye a Jamhuriyar Kongo inda ‘yan tawayen suka ƙwace muhimman birane a ƙasar.
Sakamakon zaɓen ya kasance koma baya ga babban madugun 'yan adawa Odinga, wanda ya nemi goyon bayan abokan ƙawance a cikin gida da waje.
Odinga mai shekaru 80 a duniya ya nemi shugabancin Kenya sau biyar a tsawon shekaru talatin.
Odinga ya kai ƙololuwa a siyasar Kenya inda ya riƙe muƙamin firaminista a ƙasar daga 2008 zuwa 2013.
Odinga dai ya kasance abar kauna a Kenya, sai dai wasu na ganin ƙawancen siyasarsa na baya-bayan nan da William Ruto, shugaban kasar a halin yanzu, cin amana ne na yakin neman shugabanci nagari da aka shafe shekaru da dama ana yi a kasar da ke gabashin Afirka.
Ana yawan sukar kungiyar ta AU kan rashin daukar mataki ko kuma rashin daukar matakan da suka dace kan tashe-tashen hankula a sassan Afirka daban-daban.