Tsohon Shugaban Ƙasar Senegal Macky Sall zai tsaya takarar ɗan Majalisar Dokokin ƙasar a zaɓen majalisar dokokin ƙasar da za a gudanar a ranar 17 ga watan Nuwamba.
Jam'iyyar siyasa ta Sall, the Alliance for the Republic (APR), watan cikin wata gamayya da aka shirya da sauran jam'iyyun adawa, da suka haɗa da Senegalese Democratic Party (PDS) tsohon Shugaban Ƙasa Abdoulaye Wade.
Ana kiran gamayyar Sall da suna Takku Wallu Senegal, wadda ke nufin "Ku zo mu haɗa kai don ceto Senegal" a harshen Wolof.
Gamayyar, wadda aka ƙirƙira a watan Satumba, na fatam tsira da mafi yawan kujerun majalisar dokoki mai yawan 165.
An rusa Majalisar Dokoki
Shugaba Bassirou Diomaye Faye ya rusa majalisar dokokin kasar a watan Satumba kuma ya yi kira da a gudanar da zaben ‘yan majalisar dokoki a ranar 17 ga watan Nuwamba.
Ya ce a lokacin majalisar da ke karkashin ‘yan adawa ta yi masa wahala wajen aiwatar da ajandar gwamnatinsa.
A Senegal, jam'iyyun siyasa na raba jerin sunayen 'yan takara ga hukumar zabe (CENA) gabanin zaben 'yan majalisar dokoki.
A ranar jefa ƙuri'a, 'yan ƙasa kai tsaye za su zaɓi wanda suka fi so a jerin sunayen.
Sall na kan gaba a jerin ƙawancen 'yan adawa
Bayan tattara sakamakon, jerin da suka samun mafi yawan ƙuri'u, ya dauki dukkan kujeru a gunduma.
Akwai kujeru 112 na majalisar da aka cika ta wannan hanya. Daga nan ne za a cike ragowar kujerun majalisar 53 bisa kaso na kuri'un da aka samu a kasar.
Tsohon Shugaban Ƙasar Sall ne ke kan gaba a jerin sunayen da ƙawancen Takku Wallu na Senegal ya gabatar wa majalisar.
Bibiyar gwamnati
Sall, wanda a kwanan baya ya amince da takararsa na zama dan majalisar dokoki, ya ce zai tsaya takarar majalisar ne domin ganin gwamnati ta duba lamarin.
Tsohon shugaban kasar ya ce nasarorin da gwamnatinsa ta samu musamman ta fuskar tattalin arziki, sun lalace a karkashin mulkin shugaba Faye.
Gwamnatin Faye dai ta ce ta gaji gwamnatin “da ba a yi abubuwan da suka dace ba”.
Sall mai shekaru 62 ya zama shugaban kasar Senegal na hudu daga 2012 zuwa 2024.
Sama da jam'iyyu 30 ne ke halartar zabukan
Kuri'ar raba gardama ta kasa a shekarar 2016 ta rage wa'adin shugaban kasa daga shekaru bakwai zuwa biyar, wanda za a sabunta sau daya, tun daga shekarar 2019 zuwa gaba.
Sall ya bar ofis a farkon Afrilu, lokacin da Faye mai shekaru 44 ya maye gurbinsa.
A ranar 17 ga watan Nuwamba, kawancen nasa zai fafata da jam'iyyar PASTEF mai mulkin kasar, karkashin jagorancin Shugaba Faye da Firaminista Ousmane Sonko.
Sama da wasu jam'iyyu 30 ne kuma za su shiga zaben.
Kusan masu jefa ƙuri'a miliyan 7.4
Wa'adin 'yan majalisa a Senegal sh ine shekaru biyar, ba tare da iyakance adadin lokutan da mutum zai iya tsayawa takara ba.
Yana da mahimmanci a lura cewa Sall na iya lashe kujerar majalisar dokoki, amma yana iya miƙa mukaminsa ga wani babban mamba na kawancen bisa son ransa.
Akwai kusan masu jefa kuri'a miliyan 7.4 a Senegal, kasa mai yawan mutane miliyan 18.