Kwararru kan sauyin yanayi sun alakanta bala'in da tasirin dumamar da duniya ke yi da kuma rubewar ababen more rayuwa na Libiya. Hoto: AA

Yawan mutanen da suka mutu a birnin Derna da ke kusa da gabatar teku ya kai 11,300 a yayin da ake ci gaba da ayyukan ceto bayan mummunar ambaliyar ruwan da aka yi sakamakon ruwan sama mai karfi da ya janyo ballewar wasu madatsun ruwa biyu, a cewar kungiyar agaji ta Red Crescent ta Libiya.

Marie el Drese, sakatare janar ta kungiyar agajin ta shaida wa kamfanin dillancin labarai na AP a waya ranar Alhamis cewa, an kuma ba da rahoton batan karin mutum 10,100 a birnin wanda ke kusa da Bahar Rum.

Da farko hukumomin lafiya sun ce mutum 5,500 ne suka rasa rayukansu a birnin na Derna.

Ambaliyar ruwan da kuma mahaukaciyar guguwa sun kuma yi sanadin mutuwar wasu mutum 170 din a wasu yankunan daban na kasar.

Ambaliyar ruwan ta kuma hallaka illahirin iyalai da dama a Derna a ranar Lahadi da daddare, inda lamarin ya tona asirin halin wadanda dama ke cikin kangi a kasar da ke fama da rikice-rikice tun shekarar 2011 bayan hambarar da Shugaba Muammar Gaddafi.

Shugaban hukumar jinkai ta MDD Martin Griffiths ya ce girman bala'in yana da ban tsoro da sa kaduwa.

"Wasu unguwannnin sun rushe baki daya babu su a kan taswira. Ruwa ya tafi da iyalai da dama da abin ya zo musu bagatatan. Dubbai sun mutu, dubbai sun rasa muhallansu, sannan ana ci gaba da neman wasu dubban."

Taimakon kasashen duniya

Kasashen duniya suna ta rige-rigen kai agaji Libiya tun faruwar abin.

Kasashe da dama sun kai kayayyakin agaji kamar su Aljeriya da Masar da Jordan da Kuwait da Qatar da Tunisiya da Turkiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Falasdinu.

Amurka ma ta yi alkawarin taimakawa, sannan a Turai kasashe irin su Birtaniya da Findland da Faransa da Jamus da Italiya da Romaniya duk sun kai taimako.

Sai dai ana samun matsala sosai a shiga birnin Derna saboda yadda gadoji da tituna suka lalace, sannan layukan waya ma duk sun daina aiki a mafi yawan sassan birnin, inda a yanzu akalla mutum 30,000 ne ba su da matsuguni.

Kwararru kan sauyin yanayi sun alakanta bala'in da tasirin dumamar da duniya ke yi da kuma rubewar ababen more rayuwa na Libiya.

TRT Afrika