'Yan Liberia 4,300 da ke zaune a sansanin 'yan gudun hijira na Buduburam a lardin Gabashin Gomoa da ke Tsakiyar Ghana za su koma ƙasarsu a tsakanin watannin Mayu da Yuni.
Wannan wani ɓangare ne na matakin gwamnatin Liberia na kwashe 'yan gudun hijirarta daga sansanin, ƙarƙashin Hukumar Dawo Da 'Yan Gudun Hijira ta Ƙasa, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na Ghana News Agency ya ruwaito.
A ranar Talata 21 ga Mayu ne za a fara kwashe 'yan gudun hijira 770 a motocin bas daga Ghana zuwa Liberia.
An bayyana wannan mataki ne a yayin taron ƙaddamar da kwashe 'yan gudun hijirar na Liberia tsakanin Gwamnatin ƙasar da wakilan mutanen a Budumbura.
Mista Jeddi Armah, mataimakin Ministan Harkokin Shari'a da ya jagoranci tawagar gwamnatin Liberia, ya bayyana cewa wanan mataki ne na dawo da 'yan gudun hijirar Liberia gida.
Ya ce tun shekarar 2021 mahukuntan Ghana da Liberia suka amince kan kwashe 'yan Liberia su kimanin 4,300 da ke zaune a wani sansanin 'yan gudun hijira na lardin Gomoa.
"Muna ta tattaunawa da mahukunta Ghana tsawon wannan lokaci kuma suna ba mu dukkan goyon baya da haɗin-kai don tabbatar da wannan aiki," in ji Armah.
Armah ya kuma buƙaci 'yan gudun hijirar su yi amfani da wannan dama don komawa Liberia inda tuni gwamnati ta samar da kyakkayawan yanayin komawarsu da ci gaba da rayuwa a Liberia,
Ya kuma ja hankalinsu cewa ya kamata su kalli kwashe su zuwa gida a matsayin wata sabuwar hanyar bayar da gudunmawa wajen gina Liberia da kai ƙasar babban matsayi.
Armah ya gode wa gwamnatin Ghana bisa yadda ta karɓe su hannu biyu-biyu tare da ba su haɗin kai a koyaushe.
A nasa ɓangaren Shugaban 'Yan Liberia da ke Ghana Dennis Gwion ya bayyana cewa mafi yawan su sun shirya tsaf don barin sansanin zuwa ƙasarsu, kuma wadanda za su rage su ne waɗanda suke da ƙwararan ayyukan yi da masu gidaje a wajen sansanin.
Ya ce dama ce da kashin kai da aka gabatarwa da mutane don su samu sararin komawa ƙasarsu.