Gwamnatin Nijeriya ta sanar da fara aikin kwaso 'yan ƙasarta da ke Lebanon, don dawo da su gida. Wannan mataki na zuwa ne bayan da rikici tsakanin Isra'ila da Hezbollah ke ta'azzara a Lebanon.
Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta Nijeriya, Amb. Eche Abu-Obe ne ya faɗa a wata sanarwa da aka fitar ranar Juma'a 4 ga Oktoba, 2024
Tun a Agustan 2024 ne ofishin jakadancin Nijeriya da ke Lebanon ya fitar da shawarwari ga al'ummar Nijeriya da ke ƙasar, inda ya nemi su ƙauracewa ƙasar bisa raɗin-kansu lokacin da ake iya samun tikitin jirage masu tashi.
An kwaso 'yan Nijeriya da ke kudancin Lebanon zuwa babban birnin ƙasar Beirut, da kuma sauran wurare da ke da tsaro, tare da haɗin gwiwar shugabannin 'yan Nijeriya mazauna ƙasar.
Ma'aikatar harkokin waje ta Nijeriya ta sanar da cewa babu ɗan ƙasar da ya rasa ransa tun bayan fara rikicin, kuma ta tabbatar wa da 'yan ƙasar cewa gwamnati na aiki tare da masu ruwa da tsaki don tsare rayukansu.
Ghana ta gargaɗi 'yan ƙasarta
Gwamnatin Ghana ta gargaɗin 'yan ƙasarta da ke zaune a Lebabon su gaggauta dawowa gida, ta hanyar jirgin sama na kasuwa.
A wata sanarwa da ta fitar ranar Juma'a 4 ga Oktoba, 2024, gwamnatin Ghana ta nuna matuƙar damuwarta kan ƙazancewar rikici a Lebanon, inda Isra'ila ke kai hare-hare.
Don taimaka wa 'yan ƙasar su dawo cikin aminci, ma'aikatar harkokin waje ta shawarci al'ummar Ghana da ba su da cikakkun takardun tafiya su tuntuɓi ofishin jakadancin Ghana a Alƙahira, Masar da ƙaramin ofishin jakadancin Ghana da ke Beirut.
Sanarwar ta ce “Duba da taɓarɓarewa yanayi, gwamnatin Ghana tana shawartar 'yan asalin Ghana a Lebanon su yi amfani da damar da suke da ita ta samun tikitin jirgi a Lebanon don su gaggauta barin ƙasar.
“Gwamnati na shawarata duka 'yan Ghana a Lebanon su ɗauki matakin gaggawa kan wannan shawara don kaucewa shiga matsanancin yanayi,” in ji sanarwar.