Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi gargaɗin cewa fiye da 'yan ƙasar Sudan miliyan 26 na fuskantar hatsarin yunwa./Hoto: Reuters

Cutar kwalara na ci gaba da yaɗuwa a Sudan inda ta kashe aƙalla mutum 388 sannan fiye da mutum 13,000 suka kamu da ita a watanni biyu da suka gabata, a cewar hukumomin kiwon lafiya, a yayin da yaƙin da ake yi tsakanin sojoji da dakarun rundunar ɗaukin gaggawa ya shiga wata na 17.

Cutar tana yaɗuwa a yankunan gabashin Sudan da suka yi fama da ruwan sama kamar da bakin ƙwarya a kwanakin baya inda aka yi ambaliya ruwa sannan miliyoyin mutane suke samun mafaka baya yaƙi ya raba su da muhallansu.

Kwalara ta kashe mutum aƙalla shida sannan mutum kusan 400 sun kamu da ita a ƙarshen mako, a cewar wata sanarwa da Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta fitar ranar Lahadi. An samu cutar a larduna 10 cikin larduna 18 inda ta fi ƙamari a lardunan Kassala da al-Qadarif da ke gabashin ƙasar, in ji ma'aikatar.

Mummunan yakin Sudan na ci gaba da azabtar da 'yan gudun hijira

A gefe guda, babban jami'in MDD mai kula da masu neman mafaka ya nuna damuwa kan makomar jama'ar Sudan da yaƙin basasar ƙasar ya tagayyara, yaƙin da ke ƙara jefa jama'a tafiya gudun hijira zuwa iyakokin Uganda da Turai.

Tun bayan ɓarkewar yaƙin a watan Afrilun 2023, "An kori sama da mutane miliyan 10 daga gidajensu," miliyan biyu daga cikin sun bar Sudan, Filippo Grandi ya faɗa wa kamfanin dillancin labarai na AFP a wata tattaunawa a ranar Lahadi, a yayin da ake dab da fara Babban Taron MDD.

"Mece ce makomar ƙasa irin Sudan, da yaƙi ya tagayyara?" Grandi ya tambaya.

Rawar da Grandi ke takawa ta jagorantar hukumar MDD mafi girma da ke da yawan ma'aikata 20,000, saboda ƙara yawan 'yan gudun hijira da masu neman mafaka a duniya, inda a baya-bayan nan hukumar ta lashe kambi har sau biyu.

Grandi ya ƙara da cewa akwai matuƙar damuwa ganin yadda mutane ke ƙaurace wa gidajensu, inda ya ce akwai 'yan ƙasar Sudan kimanin 40,000 a kan iyakar ƙasar da Uganda.

'Hanyoyi masu hatsari'

Grandi ya ce "Mun ga aƙalla 'yan ƙasar Sudan 100,000 sun isa Libiya."

"Mun san cewa duba da yadda ake da masu fataucin mutane da kusanci da Turai, da yawa daga cikinsu na iya yin ƙoƙarin, ko ma sun fara ƙoƙarin shiga jiragen ruwa don tsallakawa ƙasashen Turai," in ji Grandi.

Ya ƙara da cewa "Muna ta gargaɗi ga jama'ar Turai." Ya jaddada cewa babu isasshen taimakon jinƙai ga Sudan, kuma jama'ar Sudan za su ci gaba da yin ƙaura zuwa wasu ƙasashen.

"Wannan rikici ya fara yin mummunan tasiri a yankin baki ɗaya, ta hanyoyi masu hatsari."

Chadi, Sudan ta Kudu, Ethiopia, da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya wurare ne na dubban masu neman mafaka, inda Masar, ta kasance ƙasar da ke da miliyoyin 'yan gudun hijirar Sudan da dama.

Yaƙin basasar Sudan ya sanya sojojin ƙasar ƙarƙashin Janaral Abdel Fattah al-Burhan na yaƙar mayakan RSF da ke ƙarƙashin Janaral Mohamed Hamdane Daglo, inda aka kashe mutane da dama tare da jefa jama'ar ƙasar miliyan 26 cikin matsalar abinci.

'Rikici mafi muni'

An bayyana ɓullar yunwa a sansanin 'yan gudun hijira ZamZam da ke Darfur kusa da garin El-Fasher, inda a wannan makon mayaƙan RSF suka kai gagarumin hari, bayan watanni na mamaya.

"Amma mun san cewa akwai wasu tsare-tsare" - misali yadda ake danganta waɗanda ke kai hari ga ɗaya daga ɓangarorin da ke gwabza yaƙi ko kuma ma'aikatan RSF da ke ƙuntata wa fararen-hula.

Mayaƙan RSF, tare da taimakon masu tayar da ƙayar baya na ƙasashen Larabawa, sun kashe mutane tsakanin 10000 da 15,000 a garin El Geneneina na yammacin Sudan, inda ƙwararren jami'in na MDD.

Babban munin da ke tattare da rikicin shi ne - rikicin hakkokin ɗan'adam, rikicin buƙatar taimakon jinƙai - kuma har yanzu duniya ta ƙi mayar da hankali don magance rikicin.

"A ko'ina sabon rikici na korar tsohon rikici." -- daga Ukraine zuwa Gaza.

TRT Afrika da abokan hulda