Wata kungiyar 'yan ta'adda mai alaka da Al-Qaeda a ranar Talatar da ta gabata ta dauki alhakin wani hari da aka kai a filin tashi da saukar jiragen sama da kuma cibiyar horar da sojoji a Bamako, wanda shi ne hari na farko a cikin shekaru da dama da aka kai a babban birnin kasar Mali.
Kungiyar JNIM ta bayyana a tasoshinta na sadarwa cewa, an kai wani hari na musamman a filin jirgin sama na sojoji da cibiyar horar da Jandarma ta Mali da ke tsakiyar babban birnin kasar Mali da asuba.
Ta ce harin ya haifar da "asara mai yawa ta mutane da dukiya da kuma lalata wasu jiragen soji."
An yi musayar wuta mai tsanani da sanyin safiyar nan kusa da ofishin 'yan sandan da ke kula da hanyar shiga filin jirgin saman farar hula, kamar yadda jami'an tsaro da na filin jirgin suka shaida wa AFP bisa sharadin sakaya sunansu.
'An shawo kan lamarin'
Tun da farko dai rundunar sojin kasar ta Mali ta ce an shiga halin ƙaƙa-ni-kayi, bayan da ta kira yunkurin kutsawar da ‘yan ta’adda suka yi a sansanin ‘yan sanda na soji.
Hukumomin da sojoji ke yi wa jagoranci na amfani da kalmar 'yan ta'adda' wajen bayyana 'yan tada kayar baya da 'yan aware a arewacin kasar.
Har yanzu ba a fayyace girman harin da hanyoyin da aka yi amfani da su da kuma adadin mutanen da ya shafa ba, a cikin yanayin da aka takaita kwararar bayanai a karkashin mulkin soja.
Bamako dai ya kasance yana tsira daga irin hare-haren da ke faruwa akai-akai a wasu sassan kasar da ke yammacin Afirka.
'Wurare masu muhimmanci a babban birnin'
A shekarar 2016, wasu ‘yan bindiga sun kai hari a wani otel na Bamako da ke dauke da tsohuwar tawagar horar da sojojin Mali a Turai, ba tare da samun asarar rai ba a cikin ma’aikatan tawaga.
“Da sanyin safiyar yau ne wasu gungun ‘yan ta’adda suka yi kokarin kutsawa cikin makarantar ‘yan sanda ta Faladie,” in ji rundunar a shafukan sada zumunta a ranar Talata.
"An shawo kan lamarin," in ji sanarwar da aka yi a gidajen rediyo da talabijin.
Ma'aikatar tsaro ta yi magana game da "hare-haren ta'addanci" a kan "wurare masu muhimmanci a babban birnin kasar", ciki har da makarantar 'yan sanda na soja.
'Ci gaba da share su'
Hotunan da tashar talabijin ta ƙasar Mali ta watsa a baya-bayan nan, sun nuna fursunoni kusan 20, suna zaune a kasa an ɗaure musu hannaye da rufe musu idanu.
"An kawar da 'yan ta'adda. Ana ci gaba da share su," in ji babban hafsan sojojin kasar Oumar Diarra a labaran tashar ORTM, amma bai ambaci harin da aka kai a filin jirgin ba.
Nisan sansanin horar da 'yan sandan 'yan mintuna kaɗan ne daga gundumar filin jirgin sama, inda na sojojin ke maƙwabtaka da farar hula.
A wata sanarwa da ma'aikatar sufurin ta fitar ta ce an takaita shiga filin jirgin na wani dan lokaci domin daƙile duk wata barazana.
An rufe filin jiragen sama na wucin gadi
"An rufe filin jirgin saman Bamako na wani dan lokaci saboda abubuwan da suka faru," in ji wani jami'in filin jirgin, ba tare da bayyana tsawon lokacin da zai yi ba.
Wani ganau ya tabbatar wa da kamfanin dilancin labaran AFP cewa an rufe yankin kuma an kasa isa filin jirgin ta babban titin.
Hukumomi ba su sanar da adadin mutanen da abin ya shafa ba a hukumance.
Bidiyon da ba a tantance ba da ke yawo a shafukan sada zumunta na nuna gawarwaki a kasa.
Rundunar soji ta yi kira da a kwantar da hankali
Rundunar ta ce ana ci gaba da gudanar da bincike, inda ta yi kira ga jama'a da su kwantar da hankalinsu, su kauce wa yankin.
An fara jin ƙarar harbe-harbe da fashwar abubuwa da misalin karfe 5 na safe (agogon ƙasar da kuma na GMT), in ji wakilin AFP.
Har safiya ta yi ana ta jin ƙarar harbe-harbe.
Ana iya ganin baƙin hayaƙi yana tashi daga wani yanki kusa da filin jirgin.
Sun maƙale a cikin masallaci
Wani ganau ya ce shi da sauran masu ibada sun maƙale ne a wani masallaci da ke kusa da yankin a lokacin sallar asuba.
Makarantar sakandare ta Faransa, Liberte, ta sanar da cewa za ta ci gaba da kasancewa a rufe "saboda abubuwan da suka faru a waje."
Ma'aikatan tawagar Majalisar Dinkin Duniya a kasar Mali sun sami sakon cewa: "An ji karar harbe-harbe a sassan birnin Bamako. Dukkanin jami'an MDD su taƙaita zirga-zirga har sai abin da hali ya yi."
Tun a shekara ta 2012 ne kasar Mali ke fama da bangarori daban-daban da ke da alaka da kungiyar Al-Qaeda da kuma wasu kungiyoyin masu tada kayar baya, da kuma dakarun da suka ayyana kansu da kuma 'yan bindiga.