Sojojin Somaliya na ci gaba da samun gagarumar nasara kan mayakan a 'yan watannin nan. / Hoto: Reuters

Wani dan kunar bakin wake ya hallaka sojoji 13 tare da jikkata wasu akalla mutum 20 a cikin wata makarantar horas da sojoji da ke Mogadishu babban birnin Somaliya a ranar Litinin, a cewar wani soja da ya ga gawarwakin da idonsa.

Kungiyar 'yan ta'adda ta al-Shabaab ta dauki alhakin harin da aka kai da sanyin safiyar ranar Litinin a makarantar sojoji ta Jaalle Siyaad.

Wani soja a asibitin sojoji na Mogadishu wanda ya bayyana sunansa a matsayin Ahmed ya ce ya ga gawarwaki 13 da suka mutu da kuma wasu 20 da suka samu raunuka sakamakon harin da aka kai makarantar.

Wani shirin gangamin soji da dakarun gwamnati da na mayakan sa-kai suka kaddamar a bara ya kara matsa lamba ga kungiyar da ke da alaka da Al Qaeda daga yankuna da dama a kudancin Somaliya, amma duk da haka mayakan na cin karensu ba babbaka ta hanyar ci gaba da kai munanan hare-hare.

Yawan kai hare-hare

A 'yan makonnin da suka gabata yakin da sojoji ke kai musu ya tsaya cik sakamakon shirye-shirye da sojojin ke yi don kai farmaki a karo na biyu, daga lokacin ne mayakan Al-shabaab suka kara kaimi wajen kai hare-hare.

A karshen watan Mayu, sun kashe akalla sojojin da ke aikin samar da zaman lafiya na Uganda 54 a wani sansani da ke kudancin Mogadishu. Kusan makwanni biyu suka yi kawanya a Baidoa, daya daga cikin manyan biranen kasar.

Sannan a cikin wannan watan suka ci gaba da kai jerin hare-hare a Mogadishu.

"Ana kidaya sojoji ne yayin da suka yi layi a lokacin da dan kunar bakin wake ya tusa kai cikinsu ya kuma tarwatsa kansa," in ji Farah.

Adadin mutanen da suka jikkata

A wata sanarwa da kungiyar ta Al-Shabaab ta fitar ta ce harin da aka kai ya kashe sojoji 73 tare da jikkata wasu mutm 124 daban.

Kungiyar dama can ta saba bayar da alkaluman wadanda suka mutu fiye da adadin wadanda hukumomi suke bayarwa.

Tun a shekarar 2006 ne kungiyar Al-Shabaab ke yaki don hambarar da gwamnatin tsakiyar Somaliya don kafa nata mulkin "bisa tsantsar fassara da tsarin shari'ar Musulunci", kamar yadda suke ikirari.

TRT Afrika