Kungiyar bayar da agaji ta ICRC a Nijeriya ta koka kan yadda kayayyakin abinci ke yin tashin gwauron zabi a daidai lokacin da tattalin arzikin kasar ke kara tabarbarewa.
A wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar Litinin, ta bayyana cewa karuwar da aka samu ta farashin man fetur da kashi 300 sakamakon cire tallafin mai da kuma karya darajar Naira da sama da kaso 75, sun yi sanadin jawo ƙaruwa a sufurin motoci da abinci da sauran kayayyakin buƙatu.
A sanarwar, kungiyar ta ambato wani ɗan kasuwa da ke Gwoza yana cewa a baya yana sayar da buhun masara kan N40,000 amma a halin yanzu buhun ya kai 70,000.
Dan kasuwar ya koka kan cewa direbobin da ke dakon kayayyaki na korafi kan tsadar man fetur da kuma kayayyakin gyaran mota.
Haka kuma dan kasuwar ya bayyana cewa a baya sukan ci abinci sau biyu ko sau uku a rana amma a halin yanzu karin kumallo na musu wahala.
Haka kuma ya faɗi yadda aka kori ‘ya’yansu daga makaranta sakamakon sun kasa biyan kudin.
Kungiyar ta ICRC ta ce a asibitoci ana ta samun karuwar yara da ke fama da karancin abinci a arewa maso gabas.
Hauhawar farashi a Nijeriya
Wannan rahoton na ICRC na zuwa ne kwanaki bayan hukumar kididdiga ta Nijeriya NBS ta fitar da rahoton cewa hauhawar farashin kayayyaki ya kasar ta karu a watan Satumba zuwa matakin da ba a taba samu ba tsawon shekara 20 inda ya kai 26.72.
Haka kuma hukumar ta ce hauhawar farashin kayayyakin abinci zalla ta kai maki 30.64 a watan Satumba bayan an yi lissafi na tsawon shekara guda, idan aka kwatanta da yadda aka samu a Satumbar 2022 mai maki 23.34.