Gawuna

Kotun Sauraron Karar Zabe ta Jihar Kano ta sauke Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan jihar inda ta ayyana jam'iyyar APC a wacce ta yi nasara a zaben na watan Maris din 2023.

Hukumar Zabe mai zaman kanta ta Nijeriya INEC ce ta ayyana Abba Kabir a matsayin gwamna a zaben na watan Maris.

Jim kadan bayan ayyana Abba Gida-Gida a matsayin gwamna a watan Maris sai dan takarar APC Nasir Gawuna ya garzaya kotu.

Kotun mai tawagar alkalai uku ta ce a kwace shaidar cin zabe da INEC ta bai wa Gwamna Abba K Yusuf tare da umartar cewa a mika wa Gawuna ita.

Kotun ta cire kuri'a 165,663 daga kuri'un da Abba Gida-Gida ya samu inda ta ce ba su da inganci, tana mai cewa ba a mannawa kuri'un 165,663 hatimi ba don haka ba sahihai ba ne.

Yanke hukunci ta 'Zoom'

Tun da safiyar ranar Laraba aka tsaurara tsaro a Jihar Kano saboda yanke hukuncin, sannan kuma aka hana 'yan jarida da magoya bayan jam'iyyu shiga harabar kotun, wacce ke cike da jami'an tsaro.

Sannan kuma alkalan ba su je kotun ba, an saurari karar ne tare da yanke hukunci ta manhajar Zoom daga wani waje daban.

A baya alkaliyar da ke jagorantar shari'ar ta yi zargin cewa wasu lauyoyi sun yi tayin ba ta cin-hanci domin ta sauya hukuncin da za ta yanke a zaben jihar ta Kano, lamarin da ya sa aka yi ta tayar da jijiyoyin wuya.

APC ta shigar da kara

A yayin zaben da aka gudanar a watan Maris din 2023, Abba Kabir Yusuf ya samu kuri’u 1,019,602 yayin da Nasiru Yusuf Gawuna ya samu kuri’u 890,705.

Bayan da sanar da nasarar Abba Kabir da INEC ta yi sai Nasru Yusuf Gawuna ya taya shi murna tare da cewa ya rungumi kaddara.

Sai dai Jam'iyyar APC, wadda tsohon Mataimakin Gwamnan Kano Nasiru Yusuf Gawuna ya yi takara a karkashinta ta kai karar Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf na jam'iyyar NNPP kan rashin gamsuwa da sakamakon zaben gwamnan jihar.

TRT Afrika