A watan Nuwamba da ya gabata ne gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya garzaya Kotun Kolin Nijeriya don neman hakkinsa bayan Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da soke zabensa a matsayin gwamna./Hoto:OTHER

Kotun Kolin Nijeriya ta ce ranar Juma'ar nan za ta yanke hukunci kan zaben gwamnan Jihar Kano tsakanin Abba Kabir Yusuf na NNPP da Nasiru Yusuf Gawuna na APC.

Ta bayyana haka ne a wata sanarwa da ta aika wa bangarorin biyu ranar Laraba da maraice.

Lauyoyin Abba Kabir Yusuf da Nasiru Yusuf Gawuna sun tabbatar da cewa Kotun Kolin ta shaida musu cewa za ta yanke hukunci a ranar Juma'a, 12 ga watan Janairun 2024.

Bayanai sun ce Kotun Kolin za ta bari lauyoyi biyu daga kowane bangare su halarci zaman yanke hukuncin.

A watan Nuwamba da ya gabata ne gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya garzaya Kotun Kolin Nijeriya bayan Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da soke zabensa a matsayin gwamna.

Ya dauki matakin ne bayan Kotun Daukaka Kara ta tabbatar da hukuncin Kotun Sauraren Kararrakin Zabe ta Kano cewa Nasiru Yusuf Gawuna na jam'iyyar APC ne halastaccen gwamnan jihar a zaben da aka gudanar a watan Maris na 2023.

A wancan hukuncin, Kotun ta cire kuri'a 165,663 daga kuri'un da Abba Gida-Gida ya samu inda ta ce ba su da inganci, tana mai cewa ba a manna wa kuri'un hatimi ba don haka ba sahihai ba ne.

Sai dai jim kadan bayan hakan, Abba Kabir Yusuf ya shigar da kara a Kotun Daukaka Kara da ke Abuja yana kalubalantar hukuncin kotun sauraren kararrakin zaben.

Amma a hukuncinta, Kotun ta ce Abba Kabir Yusuf ba mamba ba ne na jam'iyyar NNPP a lokacin da aka gudanar da zaben 2023.

Wannan shari'a ta jawo ce-ce-ku-ce a Nijeriya musamman bayan da Kotun Daukaka Kara ta fitar da wasu takardu da wasu ke ganin sun ci karo da hukuncin da ta yanke. Ko da yake daga bisani Rajistara na Kotun ya ce hukuncinsu a bayyane yake.

TRT Afrika