Wata babbar kotun Gambia ta yanke hukuncin daurin shekara 12 ga jagoran sojojin da suka yi yunkurin kifar da gwamnatin shugaban kasar Adama Barrow a bara.
A watan Janairu aka tuhumi sojoji takwas da laifin cin amanar kasa da hada baki don kifar da gwamnati ranar 21 ga watan Disamban 2022 lokacin da suka yi yunkurin kifar da gwamnatin kasar mai mutane fiye da miliyan 2.5.
Kazalika an tuhumi fararen-hula biyu da wani dan sanda da laifin boye yunkurin cin amanar kasa da kuma hada baki wurin yunkurin kifar da gwamnati.
Sai dai kotun ta wanke mutum bakwai, ciki har da fararen-hula biyu da kuma wani babban soja daya, a yayin da ake tsaka da shari'ar.
An tuhumu wani babban soja, Sanna Fadera, wanda shi ne ya jagoranci yunkurin juyin mulkin, da laifin cin amanar kasa. Sai dai an wanke karin sojoji uku da tun da farko aka zarge su da laifi.
Ba kasafai ake samun labarin yunkurin juyin mulki a Gambia ba, kasar da take ci gaba da fama da fuskantar mawuyacin hali sakamakon bakin-mulkin tsohon shugaban kasar Yahya Jammeh.