Wata kotu a Kenya ta dakatar da Shugaba William Ruto daga dage haramcin shekara shida na sare itatuwa, wadanda suka shigar da karar sun ce wannan nasara ce ga masu kare muhalli.
Kotun Muhalli da Kasa ta umarci Shugaba Ruto da ya dakatar shirinsa na jingine haramcin sare itatuwa wanda aka yi dokar a shekarar 2018 don kare dazuka daga barzanar bacewa.
Lokacin da ya dage haramci a watan Yuli, Ruto ya ce "shirme" ne a bar manyan bishiyoyi su fara rubewa yayin da masu sarrafa itace suke shigo da itatuwa daga ketare, kuma ya ce abin da yake niyyar yi zai samar da ayyukan yi.
Kungiyar Lauyoyi ta Kenya (Law Society of Kenya) ce ta kalubalanci matakin shugaban a kotu, inda ta ce gwamnatin ba ta bayar da wata hujja a kimiyyance ba kan dage haramcin sare itatuwan ko kuma tuntubar al'umma dangane da tasirin yin haka.
Jingine fara sare itatuwan
Kotun ta "amince da bukatar kungiyar lauyoyin kasar inda ta umarce a dakatar da fara shirin," kamar yadda kungiyar ta bayyana a shafinta na Twitter ranar Laraba.
A hukuncin da ta yanke a ranar 1 ga watan Agusta, kotun ta bayar da umarnin dakatar da gwamnati daga bayar da lasisin fara sare itatuwan.
Za a ci gaba da sauraren karar a ranar 14 ga watan Agusta.
"Mun ba kotu kwararan hujjoji kuma kwarya-kwaryar hukuncin da aka yanke shi muke tsammani daga kotun," kamar yadda lauyan kungiyar lauyoyin Kennedy Waweru ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP.
Samar da kariya ga dazuka
Masu kare muhalli sun yi adawa sosai da dage haramcin kan sare itatuwa, inda suka ce ya ci karo da alkawarin da Ruto ya dauka na shuka bishiyoyi biliyan 15 don samar da kariya ga dazukan Kenya.
Sai dai shugaban kasar, wanda zai karbi bakuncin babban taro kan sauyin yanayi a watan Satumba a Nairobi, ya ce ya dukufa wajen cika alkawuran da ya dauka.
"Akwai damuwa kan daga haramcin sare itatuwa," kamar yadda ya bayyana a ranar Laraba.
"Tabbas, babu abin da zai sa mu fasa shuka bishiyoyi da muka yi shiri. Za mu tabbatar da cewa dage haramcin… bai jawo abin da muka taba gani a baya ba."
Tsohuwar bishiya
A shekarar 2018, wani kwamitin musamman da gwamnati ta kafa ya ce ana sare tsofaffin bishiyoyi a Kenya "ba bisa ka'ida ba" kuma ya yi gargadi cewa an share fili da ya kai fadin hekta 5,000 a kowace shekara.
A karar da ta shigar a gaban kotun, kungiyar lauyoyin ta ce "an riga an ma fara sare itatuwan".
Kungiyar ta ce an dage haramcin ne "ba tare da la'akari da muhimmiyar rawar da dazuka suke takawa wajen magance sauyin yanayi da kare rayuwar dabbobi daban-daban da kuma kare muhalli da sauran halittu ba."
Bangaren sarrafa itatuwa a kasar Kenya yana daukar ma'aikata 50,000 kai-tsaye da kuma wasu 300,000 wadanda ba na kai-tsaye ba ne, kamar yadda alkaluman gwamnati suka bayyana, kuma shirin dage haramcin sare bishiyoyin ya zo ne a daidai lokacin da ake fama da rashin aikinyi da hauhawar farashin kayayyaki.