Domin ta biya bashin da ake bin ta, kasar ta fito da wasu tsare-tsare uku 

Zimbabwe ta soma daukar matakai domin biyan bashin sama da dalar Amurka biliyan shida da ake bin ta a kasashen waje, wanda wannan taurin bashin ne ya sa manyan wurare irin su bankin duniya da asusun bayar da lamuni suka daina bai wa kasar da ke kudancin Afirka bashi tsawon shekara 20.

Domin ta biya bashin da ake bin ta, kasar ta fito da wasu tsare-tsare guda uku da suka hada da tsarin sauyi na tattalin arziki da na gwamnati da kuma biyan diyya ga manoma.

Halin da kasa take ciki

Daya daga cikin wani bangare na kasar da ke aiki gadan-gadan shi ma ya rushe. Harkar banki ta kasa da kasa ita ma ta ja baya kwarai inda har bankuna 102 da kasar ke kawance da su ta rasa su cikin shekara 10 da suka wuce.

A halin yanzu, kashi 90 cikin 100 na tattalin arzikin kasar na tafiya ne kara zube.

Gudunmowar da Zimbabwe ke bayarwa a matsayinta ta wata jijiya a kungiyar ci gaban kasashen kudancin Afrika ta tsaya.

Rahoton kidayar da aka yi a 2022 ta kasar Zimbabwe ya nuna cewa kusan ‘yan kasar miliyan guda na zama ne a kasashen waje, inda ‘yan kasar suka fi yawa a Afrika ta Kudumai 800,000, sannan Botswana na da 48,000 sai kuma Birtaniya mutum 23,000.

Rahoton da bankin duniya ya fitar kan tattalin arziki da kuma harkokin yau da kullum ya nuna cewa kusan rabin jama’ar Zimbabwe sun fada cikin mawuyacin hali na talauci tsakanin 2011 zuwa bara, inda akasari yara ne suka fi tagayyara.

“Ana fargabar adadin mataulata zai ci gaba da zama a kan miliyan 7.9 duk da hauhawar farashi da kuma jinkiri a samun aiki da albashi a ma’aikatu da wuraren kasuwanci,” in ji rahoton.

Dakta Akinwumi Adesina wanda shi ne shugaban bankin raya kasashen Afrika wanda bankin ne ke kan gaba wurin neman mafita ga bashin Zimbabwe, ya koka kan cewa jama’ar kasar sun sha bakar wuya.

“Akwai bukatar matasan Zimbabwe a mayar musu da kasarsu mai arziki yadda take a baya. Ba za su ci gaba da wahala kan abin da ba su suka kirkire shi ba a baya,” in ji shi.

Domin matsar da wannan lamari gaba, bankin raya ci gaban kasashen Afrika ya amince da dala miliyan 4.1 domin biyan bashi da kuma gudanar da ayyukan gwamnati.

Kasar ta koma kan tsarin biyan bashi inda akwai basusssuka sakamakon bankuna da suka hada da bankin raya kasashen Afrika da Bankin Duniya da Bankin Zuba Jari na Turai.

Sai dai kudi kalilan ake biya domin biyan wadannan basussukan duk da gwagwarmayar da gwamnati ke yi wurin biya wa yan kasa bukata.

Ra’ayin Chissano

Tsohon Shugaban Mozambique Joaquim Chissano wanda yake taka rawa a matsayin mai shiga tsakani a tattaunawar da ake yi ta warware matsalar bashin, ya bukaci duka masu ruwa da tsaki da a hanzarta tattaunawar domin ganin Zimbabwe ta zama daya daga cikin kwamitin ci gaban kasashen Afrika.

“Wannan tattaunawar mai tsari wata dama ce da bai kamata a bari ta wuce ba. Bai kamata a kashe wannan damar ba.

"Dole ne Zimbabwe ta karbi gurbinta a kungiyar SADC ta kuma jagorancin kasashen yammacin Afrika, baya ga inganta rayuwar jama’ar kasar. Kaddarar Zimbabwe na hannun 'yan kasar. Dole ne su tabbatar tana kan hanya,” in ji shi.

Bashi ga manoma farar fata

Shugaban Zimbabwe Emmerson Mnangagwa ya yi alkawarin biyan diyya ga tsoffin manoma farar fata kan inganta gonakin da aka yi.

“Biyan diyya ga tsoffin manoma bisa ga gyararrakin da aka yi wa gonakinsu da kuma cimma matsaya kan lamura da suka shafi gonaki a lokacin sauyi ga tsarin gonaki na daga cikin abubuwan da za a mayar da hankali a matsayin mataki na uku, a karkashin yarjejeniyar tallata zuba hannun jari,” in ji shi.

Tsarin hanzarta biyan kudi ya kunshi raba lokacin biyu, daga shekara 20 zuwa 10.

“A baya mun hadu a kan wani tsari na biyan manoma cikin tsawon shekaru 20. Amma a lokacin da muke ta kokarin kammalawa, sai shugabanninsu suka zo wajenmu.

"A karshe dole wani ya biya da sauri wanda zai ba mu damar biyan bashinmu cikin sauri,” in ji ministan kudi da tattalin arziki Farfesa Mthuli Ncube.

Gwamnati za ta biya dala biliyan 3.5 a matsayin diyya akasari ga manoma farar fata wadanda suka rasa gonakinsu ta hanyar shirin sauya tsarin gonaki a farkon shekarun 2000.

Ganin cewa gwamnatin Zimbabwe tana neman wasu hanyoyi na biyan diyya ga manoma farar fata, ta soke batun cewa za ta yi amfani da gonakin.

Tambayar ita ce ko za a yi amfani da gonakin a matsayin diyya? Zuwa yanzu dai babu wasu alamu da ke nuna cewa za a iya gardama a kan hakan.

“Muna nan muna neman hanyoyin tattara kudin da ake da su, kuma muna samun ci gaba ta wannan bangaren,” in ji ministan noma da gonaki da ruwa da ci gaban karkara na Zimbabwe Dakta Anxious Jongwe Masuka.

Jerin takunkumai

Karkashin jagorancin ma’aikata, akwai bukatar Zimbabwe ta kawo sauyi kan batun ‘yancin tofa albarkacin baki da kare hakkin bil adama da kuma aiwatar da dokoki bisa kundin tsarin mulki.

Zabe na gaskiya da adalci zai kuma rage wasu matsaloli da ke hanya ta bangaren biyan bashi na Zimbabwe, baya ga cire takunkuman tattalin arziki wadanda Amurka ta kakaba.

“Dole ne mu nuna ci gaba ta bangaren dimokradiyyar Zimbabwe da kuma dokar farfado da tattalin arzikin kasar wadanda dukansu za su sa a yi zabe na gaskiya da adalci.

"Wadannan kuma za su kawar da duk wata guguwa a tafiyarmu ta biyan bashi,” in ji shugaban Afdb Dr Adesina.

“Dole yan Zimbabwe su nisanci tarzoma su yi zabe cikin kwanciyar hankali na shugabanni da wakilai a gwamnati da majalisa.

Kada su yarda wani ya sauya musu tunani ko kuma su shiga wani rikici ko wani aiki mara kyau da zai iya kawo cikas ga zabe. Dole ne su zama a ankare su yi zaben gaskiya da adalci.” Kamar yadda tsohon shugaban Mozambique Chissano ya bayyana.

Wasu daga cikin ka’idojin da aka bayar na cire ZIDERA sun hada da sojoji su nesanci siyasa da kyakyawan gudanar da gwamnati da bayar da girma ga ‘yan adawa da biyayya ga doka da hakkin bil adama.

Jobst von Kirchmann wanda shi ne jakadan Kungiyar Tarayyar Turai a Zimbabwe ya ce yana da yakinin cewa kasar za ta ci gaba ta tafarki mai kyau.

“Abin da muke son cimmawa shi ne kowa ya samu nasara. Akwai bukatar a amince a wani da wani tsari na tuntubar juna.

"Tsarin sa ido kan ma’aikata na IMF shi ne na farko sa’annan kyakkyawar gwamnati ita ce ta biyu, sakamakon hakan a matsayin wani mataki na nuna cewa du kana da yakini kan cewa Zimbabwe na tafiya kan tafarki mai kyau.

"Abin da za mu iya a matsayinmu na kawaye domin mu tallafa wa shirin za mu yi.”

TRT Afrika