Kenya ta karbi baƙuncin jami'a  'mafi girma' a duniya da ke yawo a teku

Kenya ta karbi baƙuncin jami'a  'mafi girma' a duniya da ke yawo a teku

Jirgin ruwa mai suna MV World Odyssey yana ɗaukar ɗalibai don yin karatun zangon karatu a teku.
Jami'ar, wacce aka fi kiranta da "jami'a mafi girma da ke kan teku", ta saba ziyartar Kenya tun daga shekarar 2022.

Wani katafaren jirgin ruwa da yake aiki a matsayin jami'a ya isa birnin Mombasa da ke gaɓar teku a ƙasar Kenya, kamar yadda hukumomin kula da tashoshin jiragen ruwa na ƙasar suka faɗa.

Jami'ar mai yawo a cikin teku, wacce ke ƙarƙashin kulawar Cibiyar Ilimi ta Jiragen Ruwa, ya shiga birnin Mombasa ne a ranar Juma'a, 9 ga watan Fabarairu, kuma zai shafe kwana shida a can.

Jirgin ruwan na MV World Odyssey wanda aka saka wa suna “Semester at Sea” yana ɗaukar ɗaliban jami'a da ke karatun digiir na farko da waɗanda suka kammala jami'a kwanan nanda sauran ɗalibai don su shafe tsawon zango guda a kan teku, lamarin da ya haɗa da zaaya ƙasashe da dama a duniya don koyon tarihi da al'adu.

"Akwai fasinjoji 763 a cikin jirgin ruwan, waɗanda 585 daga cikinsu ɗalibai ne da za su ziyarci wasu cibiyoyin ilimi da kai ziyara birane da gandun namun daji da dama a yayin zaman nasu, a matsayin yawon buɗe ido na ilimi.

Jami'ar, wacce aka fi kiranta da "jami'a mafi girma da ke kan teku", ta saba ziyartar Kenya tun daga shekarar 2022.

Tashar jirgin ruwa ta Mombasa ta samu ƙarin yawan kira daga jiragen ruwan da ke son zuwa, inda tashar ta samu baƙuncin fasinjoji 2,500 na jirgin ruwan MSC Poesia, ɗaya daga cikin manyan jiragen ruwan da suka kira tashar a ranar Asabar, 3 ga watan Fabrairu.

TRT Afrika