Kamfanonin lantarkin na Ghana su ke samar da sama da rabin wutar da ake amfani da ita a kasar. Hoto/AP

Kamfanoni masu zaman kansu da ke samar da wutar lantarki a Ghana sun dakatar da yajin aikin da suka yi niyyar tafiya tsakanin 1 zuwa 8 ga watan Yuli.

Kamfanonin wadanda su ne ke da kashi 50 cikin 100 na hannun jari a samar da wutar lantarkin kasar na bin gwamnatin kasar kusan dala biliyan biyu.

Hakan ne ya sa tun da farko kamfanonin suka yi niyyar yanke wutar lantarkin kasar idan gwamnatin ta Ghana ta gaza biyan akalla kashi 30 cikin 100 na kudin.

Kamfanonin lantarkin kasar masu zaman kansu wadanda su tara ne sun dakatar da yajin aikin da suka kudiri aniyar shiga bayan sun tattauna da kamfanin lantarki na Ghana ECG a ranar Juma’a.

Kamfanin lantarkin kasar ya amince da biyan kamfanonin wani kaso daga kudin wanda ba a bayyana ba domin ba su damar gudanar da aiki na wucin gadi, wanda hakan zai ba gwamnatin kasar damar samun karin kudi.

Sai dai babu tabbaci kan tsawon lokacin da aka cimma matsaya na biyan sauran kudin tsakanin gwamnatin kasar da kuma kamfanonin lantarkin.

Babban kalubale

Da a ce wadannan kamfanoni sun shiga yajin aikin da suka yi niyya, da hakan ya jefa sassa daban-daban na kasar Ghana a cikin duhu, sakamakon kamfanoni masu zaman kansu na kasar ke samar da kashi 67 cikin 100 na wutar lantarki a kasar tare da iko da rabin lantarkin da ake samarwa.

Tsohon shugaban Ghana John Dramani Mahama ya bukaci kamfanonin wadanda ke samar da megawatts 2,000 da su dakatar da yajin aikin da suka yi niyyar shiga tare da tattaunawa da gwamnati.

Mahama ya bukaci kasar ta Ghana da ta yi kokarin biyan bashin da ake bin ta domin kauce wa abin da kin yin hakan zai iya jefa kasar idan aka yanke wutar kasar na mako guda ko kuma sama da haka.

TRT Afrika